Ko dai Arewa ce kaɗai Nijeriya?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Tambayar da kwanan nan ke shigowa dodon kunne na ita ce “Shin Arewa ce kaɗai Nijeriya?.” Amsar tambayar na buƙatar a duba abu uku, na farko tarihin haɗe kudanci da arewacin Nijeriya a 1914 da yadda gimbiyar Babban Gwamna Lord Luggard ta raɗa wa Nijeriya sunan. Na biyu za a duba yadda wasu sassan masar ke cewa su na son ɓallewa don kafa ƙasar kan su duk da ba kowa ne ke da ra’ayin ba. Na uku za a duba yadda ‘yan Arewa su ka sadaukar da kai wajen yaƙin basasa har dakaru su ka ci galabar ‘yan Aware a 1970.

Ga tarihin haɗuwar Nijeriya ya biyo bayan yadda Turawan mulkin mallaka su ka mulki yankunan Nijeriya biyu da bambancin salo. A yayin da su ka mulki kudanci kai tsaye don mutan kudun na son zama baƙaƙen Turawa, lamarin ba haka ya faru a Arewa ba don Turawan sun mulki yankin ta hanyar gwamnatin sarakuna. Ita kuwa uwargidan gwamna Lugga, wato Flora Shaw da asalin ta ‘yar jarida ce ta yi nazari inda ta ƙirƙiro sunan Nijeriya wato yankin kogin Neja don kowa ya amfana.

Su kuwa masu kamfen ɗin ɓallewa daga ƙasar na nuna tamkar suna faɗa da ‘yan Arewa ne don yadda su kan yi kisan gilla ga ‘yan Arewan da kwana ya ƙare. Abu na uku sadaukar da kai da ‘yan Arewa su ka yi ƙarƙashin manyan hafsoshin soja ‘yan asalin yankin irin su Janar Yakubu Gowon, Janar Murtala Muhammed, Janar Mamman Shuwa da sauran su na nuna ‘yan Arewa ke kishin zama a dunƙulalliyar Nijeriya.

Ƙaddara ma ba a yi yaƙin basasa ba, wa zai haɗa kan Nijeriya? Anya da ba tun tuni a na da wajen ƙasashe uku daga ƙasar ba kuwa mafi yawan baƙar fata a duniya? Haƙiƙa inda ‘yan Arewa sun yi kwanciyar magirbi a lokacin da yau ba wannan Nijeriya da wasu ke neman wargazawa.

Matsayar da gwamnonin kudancin Nijeriya su ka fitar ta shugabancin Nijeriya a 2023 ya koma yankin su na jawo muhawarar muradin gwamnonin da kai tsaye ya shafi jam’iyyar APC mai mulki ban da PDP mai adawa.

A zahiri alamu na nuna jam’iyyar da ke mulki ta fi tagomashin samun lashe zabe fiye da ta adawa da hakan kan sa hankali ya koma kan ta a lamuran mulkin karɓa-karɓa da babu shi cikin tsarin mulkin ƙasa.

Gwamnonin waɗanda kan haɗe kai su yi taro ba tare da bambancin jam’iyya ba, kamar yadda suka yi a kwanakin baya a Asaba jihar Delta wajen ɗaukar matakin haramta kiwo da ‘yan Arewa ne ke yi a dazukan yankin su. Kuma ko da makiyayin ma a can a ka haife su ko ma a ce wasu tun kakanin su, amma hakan ga ɗan Kudu ba ya sake wa tuwo suna.

Zuwa yanzu ba haƙiƙanin bayani ko matsayar APC ga sashen da zai karɓi tikitin jam’iyyar yayin da shugaba Buhari ke kammala wa’adi.

Manyan ‘yan jam’iyyar musamman daga Arewa na nuna ya fi dacewa a biye wa cancantar ɗan takara fiye da yankin da ya fito. A wata zantawa da ɗan’uwan Shugaba Buhari wato Malam Maman Daura ya bayyana irin wannan ra’ayi na duba cancanta wajen lamuran zaɓen shugabancin Nijeriya. Shi ma wani shaharerren dattijo a Arewa Hussaini Gariko daga Jihar Jigawa ya ƙara ma nuna tarihin yadda rabon mulki da arziki ya ke a Nijeriya ya na mai cewa matuƙar mulki ya bar yankin Arewa musamman ya koma hannun masu adawa da yankin to sai yadda hali ya yi.

Da a ka kara tambayar sa shin zaman mulki a Arewa na taimaka wa talakawa ne ko ‘yan jari hujja? Gariko ya ce aƙalla ko mutunta mutum mai sanya riga da hula irin wacce shugaba Buhari ke sakawa a fadar Aso Rock ta isa abar misali na tasirin mulki ga jama’a.

Jam’iyyar PDP mai adawa ta yi nasarar gwada wanan tsari na karɓa-karɓa a 2007 inda bayan rasa nasarar tazarcen tsohon shugaba Obasanjo, ta kawo tikiti Arewa inda marigayi shugaba Umaru Musa ‘Yar’adu ya zama shugaba amma cikin ikon Allah mulkin ya koma kudu sanadiyyar rasuwarsa.

Wani dai dace a wancan lokacin shi ne kamfen ɗin da ‘yan yankin Kudu maso Kudu ke yi cewa ɗan yankin su bai taɓa mulki ba, ya zo da rantsar da Goodluck Jonathan wanda ya sake dawowa a 2011 ya kuma sake gwadawa a 2015 amma sai shugaba Buhari daga Arewa ya samu nasara. Manyan sassan Nijeriya sun hau karagar mulki wa imma a soja ko farar