‘Yan bindiga sun kashe mutum 39 a harin ramuwar gayya a Zamfara

Daga SUNUSI MUHAMMAD, a Gusau

Aƙalla mutane 39 ne ‘yan bindiga suka kashe a wani harin ramuwar gayya a Faru da ke ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

A wata tattaunawa ta wayar tarho da wani mazaunin Faru mai suna Malam Lawali Ahmad Faru, ya ce, “‘Yan bindigar sun afka wa garin ne da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar Alhamis inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi da bindigogi a cikin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, wanda hakan ya yi ajalin mutane 39 wanda galibinsu maza ne.”

Ya ce ‘yan taddan sun bi manoma har hona inda suke aiki suka buɗe musu wuta yayin harin.

A cewarsa, harin ‘yan taddan daukar fansa ne, bayan kamawa da kashe wasu ‘yan ta’adda biyu da ƙungiyar ‘yan banga da aka fi sani da ‘Yan sa-kai suka yi a kan hanyar Mafara zuwa Faru waɗanda aka kama da bindigogi ƙirar AK-47 biyu a ranar Larabar da ta gabata.

“Kamar yadda nake magana da ku a yanzu, an ajiye gawarwakin mutanenmu 39 da ‘yan taddan suka kashe a Faru Primary Health Centre bisa kulawar sojoji da sauran jami’an tsaro don binne su kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar a safiyar yau, haka kuma tuni mutanenmu sun tafi daji neman waɗanda ‘yan bindiga suka kai ma hari yayin da suke aiki a gonakinsu daban-daban,” in ji Lawali.

Jami’in Julɗa da Jama’a na ’Yan Sandan Jihar, SP Muhammad Shehu, ya tabbatar wa wakilinmu da da aukuwar lamarin, yana mai cewa mutane 35 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da wasu mahara da suka kai a yankin da lamarin ya shafa.

Shehu ya ce, “Tuni aka tura rundunar tsaro ta haɗin gwiwa da ta ƙunshi sojoji da ‘yan sanda da NSCDC zuwa yankin kuma an dawo da zaman lafiya a yankin nan take”.

Tuni dai aka yi wa marigayan nana’iza daidai da karantarwar addinin Musulunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *