Ko mace na da damar sakin mijinta? (1)

Daga AISHA ASAS

Na san da yawa za su yi mamakin wannan darasi na mu, musamman ma maza da za su ga abin kamar cin fuska, kasancewar saki ɗaya daga cikin ababen da suke tinƙahon su kaɗai ke da iko kan sa.

Kasancewar darasin na mu na yau tambaya, za mu fara da amsa ta, domin kawar da kwankwanton da mai karatu yake ciki. Amsar kuwa ita ce, mace na da damar sakin mijinta, sai dai ba irin damar da mijinta ke da kan ta ba.

Na san za ku ce Asas ta zo da wani sabon al’amari, sai dai ko kaɗan ba sabo ba ne, domin daɗaɗɗen hukunci ne da ya jima tamkar yadda sakin da miji zai ma matarsa yake.

A lokacin da namiji ya bayar da sadaki ga waliyan wadda yake son ta zama matarsa, bayan cika sharuɗɗan aure, ta zama matarsa, addini ya ba shi riƙon yagiya uku na auren, waɗanda auren ke rayuwa akan su, idan sun tsinke, to auren ya tsainke. Waɗannan yagiyoyin aka ce yana da damar tsinke su idan ya so, wanda shi ne saki. Ya saki yake kasancewa, shi ne furuci daga bakinsa zuwa kunnenta ko na waliyinta, ko a rubuce “na sake ki,” wannan furucin ne zai iya kwance ƙullin da aka ɗaura tsakanin ma’aurata.

Abin tambaya anan idan ba haka addini ya ba wa mace damar sakin mijinta ba, ya nata sakin yake?

Idan ba mu manta ba, miji yakan bada dukiya da zai zama tukaici ga mallakar mace wanda shine sadaki, kuma mace ke da haƙƙi kan wannan dukiya, domin malamai sun tabbatar ba a halastawa kowa dukiyar ba sai wanda ta ba wa, ko da iyaye ne, kuma wannan dukiya takan zama tata ne idan miji ya kusanceta, to koda rabuwa suka yi ba shi da halin neman wannan dukiyar ko da kuwa dare ɗaya suka yi tare, matuƙar ya kusance ta.

Kazalika shi ne mai neman wurin zama, hidindimun auren da kuma kula da buƙatun matar, don haka adalci ne ace shi aka ba wa riƙon waɗannan yagiyar, don zai fi sanin zafin su. Sai dai hakan bai hana Musulunci yi wa macen adalci ba, domin lokuta da dama abin da ya sa miji son rabuwa da matarsa, ita ma matar yakan iya zama buƙatarta. Idan kuwa bata da wata mafita idan hakan ta samu, ɓarna zata iya shiga, har a kai ga nadama. Wannan ta sa aka bata dama ɗaya da za ta iya kuvucewa yagiyar ko da shi mijin bai so hakan ba. Wannan shi malamai ke kira da ‘Hulu’I’.

Me ake nufi da Hulu’i? wata dama ce da aka ba wa mace don fansar kan ta daga ɗauraren aurenta. Kamar yadda muka faɗa a makon da ya gabata, cikin dalilin da ke kawo saki akwai miji ya wayi gari ya daina sha’awar matarsa, wannan dalilin zai iya kawo saki. Wannan kan faru da ita kanta mace, idan ta wayi gari ta daina sha’awar mijinta, ko tana shan azabtarwa a zaman, ko qarfin sha’awarta ta fi ta sa, ko yafi ƙarfin tata, duk waɗannan suna iya zama sanadin fitar auren a ranta, kuma don waɗannan matsalolin aka tanadi hulu’i.

Ya ake yin wannan saki na hulu’i? akan yi wannan a gaban alƙali ko wasu shedu, kamar iyaye. Yayin da mace ta ƙuduri rabuwa da mijin da ya sauke haƙinta na ci, sha, sutura da kuma biyan buƙata, to za ta ba shi wani abu daga dukiya, wanda shi zai iya samun damar maye gurbinta da wata, ma’ana sadaki, a wannan lokacin wasu malamai ke ganin ba sadaki kawai ba, har da ɗan abin da zai yi hidimar auren ko da ba da yawa ba. Misali, idan dubu ashirin za a bayar don sadaki, sai a nemi ta bayar da dubu hamsin, don ya samu ya yi auren ba tare da matsala ba. Wasu kuwa suka ce akan duba yanayin matar da kuma dalilin buƙatar rabuwar a sa abinda ya dace.