Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Rahotanni sun ce ƙungiyar Paris St-Germain ta bai wa Kylian Mbappe wa’adin sabunta kwantiragi a ranar 1 ga watan Agusta ko kuma ya bar ƙungiyar.
Ana raɗe-raɗin cewa ɗan wasan na Faransa, mai shekara 24, ya amince ya koma Real Madrid a kakar wasa mai zuwa a kyauta idan kwantiraginsa a PSG ya ƙare.
Mbappe na damar barin PSG a kakar bana – ko dai a matsayin aro ko kuma a kan kwangilar dindindin, wanda ta hakan ne PSG za ta iya samun kuɗi a kansa.
Sai kuma yanzu ga Chelsea da Barcelona na nuna sha’awar ɗaukar ɗan wasan.
A cewar wata majiya, mamallakin Chelsea, Todd Boehly, yana son Mbappe amma yana fuskantar gogayya daga Barcelona inda ƙungiyoyin biyu ke da niyyar bayar da ’yan wasa da kuma tsabar kuɗi.
