Koriya ta Arewa ta janye daga gasar Olympics saboda tsoron cutar korona

Daga WAKILINMU

Koriya ta Arewa ta bada sanarwar ba za ta halarci gasar Olympics da aka shirya gudanarwa a Ƙasar Tokyo ba a cikin wannan shekara saboda dalili na neman kare ‘yan wasanta daga kamuwa da cutar korona.

Koriya ta Arewa ta ce na musamman ta ɗauki wannan mataki domin kare ‘yan wasanta gudun kada su harbu da cutar korona.

Wannan mataki da ƙasar ta ɗauka ya katse wa Koriya ta Kudu damar da ta hango na yin amfani da gasar wajen tattaunawa da takwararta Koriya ta Arewa game da abin da ya shafi kan iyaka.

A 2018 ƙasashen biyu sun shiga gasar Olympics ta lokacin sanyi wanda hakan ya haifar da aukuwar wasu abubuwa waɗanda tarihin ƙasashen biyu ba zai manta da su ba.

Pyongyang ta ce ba ta da waɗanda suka kamu da ƙwayar cutar korona amma masana sun ce hakan ba mai yiwuwa ba ne. Ana tunanin tsarin kiwon lafiyar ƙasar ba shi da ingancin yaƙi da annobar ta korona, kamar dai yadda BBC ta ruwaito.

Duba da wannan matsaya da Koriya ta Arewa ta ɗauka, ya sanya ƙasar ta zama fitacciyar ƙasa ta farko da ta bayyanar da cewa ba za ta samu halartar gasar Olympics ba saboda annobar korona. Ya zuwa 23 na Yuli mai zuwa ne ake sa ran soma gudanar da gasar.

Wannan shi ne karon farko da Koriya ta Arewa ba za ta halarci wasannin Olympics na bazara ba tun 1988, lokacin da ta ƙaurace wa wasannin Seoul yayin yaƙin cacar baki.

Tun bayan ɓarkewar annobar korona a ƙasar a shekarar da ta gabata, Koriya ta Arewa ta ɗauki tsauraran matakai wajen yaƙi da ita, ciki har da rufe iyakokinta da dai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *