
Daga BELLO A. BABAJI
Alƙali Obiora Egwuatu na Babbar Kotun Tarayya dake Abuja, ya ɗage sauraron ƙarar da Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar akan Majalisar Dattawa zuwa ranar 25 ga watan Maris.
A cikin ƙarar, Natasha ta nemi kotun da ta haramta wa kwamitin ladabtarwa na majalisar yin bincike akan ta.
A makon da ya gabata ne kotun ta bada umarnin, wanda daga bisani sai da majalisar ta dakatar da Sanatar na wata shida bayan karɓar rahoton kwamitin.
Bayan nazarin kan jawaban da lauya mai kare ɓangaren Sanata Natasha ya gabatar wa kotun, Alƙali Egwuatu ya tabbatar da su.
Sannan, sai lauya mai kare ɓangaren Sanata Godswill Akpabio, Kehinde Ogunwumiju ya roƙi kotun da ta ɗaga batun sauraron ƙarar zuwa wani lokaci don a ba su damar tattaro bayanansu.
Alƙali Obiora Egwuatu ya ɗaga sauraron ƙarar zuwa ranar 25 ga watan Maris, ya na mai umartar a tanadi duk wani abinda ake buƙatar gabatarwa kafin ranar.
