Kebbi: Lakurawa sun kashe mutane 13 da ƙone ƙauyuka takwas yayin ramuwar kisan Mai-Gemu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A wani yunƙuri na ramuwa kan kisan shugabansu Mai-Gemu da jami’an tsaro suka yi, a ranar Lahadi ne mayaƙan Lakurawa suka kai hari a ƙauyen Birnin Dede a Jihar Kebbi, inda suka kashe mutane 13.

Wani shaida ya ce, ƴan ta’addar sun kuma cinna wa ƙauyuka takwas da ka kusa da inda suka yi kashe-kashen duk a Ƙaramar Hukumar Arewa ta jihar.

Ya bayyana cewa, mayaƙan sun kai harin ne a hali na ramuwa ga kisan jagoran nasu da jami’ai suka yi.

Ya ƙara da cewa, ƙauye ɗaya ne kaɗai maharan ba su kai hari ba sakamakon kewaye shivda jami’ai suka yi.

Shugaban ƙaramar hukumar, Sani Aliyu ya tabbatar wa manema labarai aukuwar lamarin.

A kwanan nan ne jami’an tsaro na haɗin-gwiwa suka kashe jagoran ƴan ta’addar a ƙoƙarin su na daƙile ayyukan ta’addanci a jihar.

By Babaji