
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaban Jam’iyyar APC a Ribas, Tony Okocha, ya yi kira ga Gwamna Siminalayi Fubara na jihar da ya sauka daga kujerarsa ko kuma a tsige shi.
Ya bayyana hakan ne a safiyar ranar Litinin, a lokacin da Fubara ya gayyaci ƴan majalisar dokokin jihar guda 27.
A yayin ganawa da manema labarai, Okocha ya ce, ta kowacce fuska, Fubara ya yi rashin girmamawa ga Shugaba Bola Tinubu da cin mutuncin dokar ƙasa, ya na mai bada misali da sadda Shugaban ƙasa ya tsoma baki a farkon rikicin a 2023 da kuma yin karan-tsaye ga hukunce-hukuncen kotu.
Ya kuma ce, duk da cewa Fubara ya gayyaci ƴan majalisar, hakan ba zai yi tsari ga hukuncin Kotun Ƙoli ba, inda ya ce a yanzu zaɓi biyu gwamnan ya ke da su – ko dai ya yi murabus ko kuma a tsige shi.
A Majalisar Dokokin jihar kuwa, jagororinta ɓangaren Martins Amaewhule ne suka gudanar da zama a yau Litinin inda daga cikin manyan batutuwan da suka tattauna akwai ƙin amsa gayyatar gwamnan, gabatar da kasafi da sauransu.
Hakan ya nuna cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba game da rikicin siyasa a jihar.
