Nasir El-Rufai ya fice daga jam’iyyar APC, ya koma SDP

Daga USMAN KAROFI

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) bayan shekaru masu yawa na kasancewa ɗaya daga cikin ya’yan jam’iyyar. El-Rufai ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne saboda rashin ganin ci gaba a tafiyar jam’iyyar, wanda ya ce ta kaucewa manufar asali da aka kafa ta a kai.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin sa na Facebook a yau, 10 ga Maris 2025, El-Rufai ya ce yana jin takaici ganin yadda APC ta canza akalar tafiyarta cikin shekaru biyu da suka gabata, duk da irin gudunmuwar da ya bayar wajen tabbatar da nasarorin zaɓen shekarun 2015, 2019 da 2023. Ya kuma bayyana cewa yana da ƙwarin gwiwa kan irin nasarorin da ya samu a Jihar Kaduna, musamman a fannin ilimi, kiwon lafiya, gina ababen more rayuwa da samar da guraben aiki.

El-Rufai ya ce ya ɗauki matakin ficewa daga APC ne bayan kammala tuntuɓa da manyan masu ruwa da tsaki, abokan siyasa da magoya bayansa daga sassa daban-daban na ƙasar. Ya bayyana cewa ya yanke shawarar komawa jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) domin ci gaba da fafutukar tabbatar da manufofin ci gaba da dimokuraɗiyya da yake goyon baya.

Ya kuma yi kira ga magoya bayansa da sauran masu kishin ƙasa da su marawa tafiyar SDP baya domin haɗa kai da sauran jam’iyyun adawa wajen ƙalubalantar APC a duk zaɓukan da za a gudanar daga yanzu zuwa shekarar 2027. El-Rufai ya ce zai yi aiki tuƙuru wajen haɗa kan ‘yan adawa domin samun damar ceto Najeriya daga halin da take ciki.