Kotu ta ba Jonathan damar sake tsaya wa takara

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bai wa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, damar tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027. Hukuncin ya zo ne bayan shari’ar da aka shigar domin hana shi sake neman kujerar shugaban ƙasa.

Wani mutum mai suna Johnmary Jideobi ne ya nemi kotu ta hana Jonathan gabatar da kansa ga kowace jam’iyya a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa. Haka kuma ya buƙaci a hana INEC karɓar sunansa ko wallafa shi a matsayin ɗan takara.

Sai dai a hukuncin da Mai Shari’a Peter Lifu ya yanke ranar Talata, kotun ta bayyana cewa Jonathan na da damar shiga takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027. Kafin wannan hukunci, wani bangare na jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki ya bayyana Jonathan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa ɗaya tilo na ɓangaren.

Jonathan ya taɓa shugabancin Najeriya daga shekarar 2010 zuwa 2015 kafin ya sha kaye a hannun tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a zaɓen shekarar 2015. Shi ne shugaban ƙasa na farko a tarihin Najeriya da ya faɗi zaɓen sake komawa mulki yayin yana kan karagar mulki.

By ukarofi