Kotun tarayya da ke zaune a Legas ta ba da umarni ga hukumar kula da watsa labarai ta ƙasa (NBC) da ta dakatar da amfani da dokar NBC da Kundin watsa labarai na Nijeriya wajen ƙaƙaba wa gidajen watsa labarai tarar kuɗi, barazana da takunkumi, tare da tsoratar da su. Alƙalin kotun, Mai Shari’a Nicholas Oweibo, ya yanke hukuncin cewa “NBC da ma’aikatanta ba su da hurumin ƙaƙabawa gidajen watsa labarai hukunci ba bisa ƙa’ida ba, ciki har da tara, dakatarwa, ko janye lasisin aiki, ko kuma wani nau’i na hukunci da zai tauye ‘yancin gidajen labarai na samun damar watsa bayanai.”
Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da cibiyar kare hakkokin jama’a da shugabanci (SERAP) da cibiyar bunƙasa kafar watsa labarai (CJID) suka shigar a kotun, inda suka nemi a hana NBC ɗorawa gidajen labarai tara da takunkumi. A shekarar 2022, NBC ta ɗorawa kamfanonin Trust TV, Multichoice Nigeria Limited, NTA-Startimes Limited, da TelCom Satellite Limited tarar kuɗi na Naira miliyan biyar kowannensu kan wasu finafinai da suka nuna abubuwan da suka shafi yan ta’adda a ƙasar. NBC ta bayyana cewa fina-finan sun ɗaukaka ayyukan ‘yan bindiga, sun kuma kawo naƙasu ga tsaron ƙasa da kuma saɓawa kundin watsa labarai na Nijeriya.
A cikin hukuncin da ya yanke, Mai Shari’a Oweibo ya bayyana cewa “SERAP da CJID suna da hurumin shigar da ƙarar a kan wannan batu, domin wannan lamari ne mai muhimmanci ga jama’a.
Kotun ta kuma yanke hukunci kan cewa duk wani matakin hukunci da NBC ta ɗauka, ciki har da ƙaƙaba wa gidajen watsa labarai tarar kuɗi, ya saɓawa dokar Nijeriya da kundin tsarin mulki tare da take dokar Afirka ta Kare haƙƙoƙin ɗan Adam da kuma yarjejeniyar kare haƙƙin jama’a ta duniya. Saboda haka, kotun ta dakatar da tarar Naira miliyan biyar da aka ƙaƙabawa Trust TV da sauran kamfanonin watsa labarai. Kotun ta kuma hana NBC ɗaukar matakin ɗorawa kowanne gidan labarai mai zaman kansa takunkumi, dakatarwa ko wata barazana ga aikin watsa labarai a ƙasar.
SERAP ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya umurci ma’aikatar labarai da al’adu, ofishin lauyan gwamnati da NBC da su girmama hukuncin kotun. Kolawole Oluwadare, mataimakin daraktan SERAP, ya ce “Mun yi kira ga NBC ta yi biyayya ga doka ta hanyar mutunta wannan hukuncin kotu ba tare da wani jinkiri ba.” Haka kuma, ya buƙaci NBC da ta bayyana cikakken bayani kan yarjejeniyar da aka cimma da Twitter kamar yadda kotu ta buƙata.
A shekara ta 2022, SERAP da CJID sun shigar da ƙara kan tsohon Shugaba Muhammadu Buhari da tsohon Ministan Labarai, Lai Muhammed da NBC, inda suka nemi kotu ta soke ƙaƙaba tara ba akan ƙa’ida ba.
