Gwamnan Neja ya yi jimamin rasuwar babban limamin Minna

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya yi alhinin rasuwar babban limamin Minna, Malam Ibrahim Isa Fari.

Gwamnan wanda ake masa laƙabi da ‘The Farmer Governor’, wato Manomin Gwamna, ta ofishin Sakataren Labaransa, Bologi Ibrahim, ya bayyana mutuwar limamin a matsayin abin baƙin ciki ga jihar da ma al’ummar Musulmi baki ɗaya.

Ya ce marigayin ya kasance mutumin kirki da ke yawan yin wa’azi game da soyayya da haɗin-kai wanda kuma ya rayu bisa sadaukarwa ga Musulunci da za a yi kewarsa acikin al’umma.

A lokacin da ya ke miƙa gaisuwar ta’aziyyarsa ga Masarautar Minna da iyalan mamacin, Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya sanya shi cikin Aljannar Firdausi.

Ya kuma yi fatan ƴan uwa da abokan arziƙin mamacin su ɗauki dangana game da babban rashin.

By Babaji