Zaɓen gwamnan Ondo: Ɗan takarar APC ya yi fintinkau a ƙananan hukumomi 15

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jam’iyyar APC na gaf da lashe zaɓen gwamnan Ondo sakamakon samun gagarumar nasara a ƙananan hukumomin jihar da ya ke yi.

Kawo yanzu, sakamakon da hukumar zaɓe, INEC ta sanar, ɗan takarar APC’n ya yi fintinkau a ƙananan hukumomi 15.

A halin yanzu, Aiyedatiwa ne akan gaba da ƙuri’u 301,113 yayin Agboola Ajayi na jam’iyyar PDP ke bi masa da ƙuri’u 97,041.

Ana sa ran kammala ƙirga ƙuri’un zaɓen a yau bayan da hukumar ta tafi hutu inda ta ce za ta cigaba da sanar da sakamakon da misalin ƙarfe sha biyu na rana.

By Babaji