
Daga BELLO A. BABAJI
Babbar Kotun Tarayya dake Fatakwal a Jihar Ribas ta fitar da umarnin hana ƴan sanda da DSS da wasu hukumomin tsaro kama Edison Ehie, wanda shi ke dakataccen shugaban mai’aikatan gwamnatin Siminalayi Fubara.
Hakan ya biyo bayan ƙara da Ehie ya shigar ne a kotun, wanda Alƙali IPC Igwe ya yi hukunci a kai.
Sauran waɗanda ya zayyano sunayensu a ƙarar sun haɗa da Sufeton Janar na ƴan sanda, Darakta-Janar na Hukumar DSS da Daraktan DSS na jihar da kuma Hukumar Kula da ƴan sanda (PSC).
Alƙalin ya haramta wa waɗanda aka zayyano ko jami’ansu kama wanda ya shigar da ƙarar ko gayyatar sa da sunan bincike ko dukkan wani nau’i na tozarta shi.
Ya kuma umarce su da su kiyaye hukuncin har zuwa lokacin da za sake tada batun.
Daga nan ne alƙalin ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 30 ga watan Afrilu, 2025.
