
Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe
Shugaban Kwamitin Hulɗa da Al’umma na ‘Yan Sanda (PCRC) reshen jihar Gombe, Kwamared Garba Muhammad Ubale, (Kainuwan Akko), ya yi kira ga al’umma da su bada cikakken goyon baya ga ‘yan sanda ta hanyar samar da bayanai masu muhimmanci da za su taimaka wajen tabbatar da tsaro.
Kwamared Garba Ubale ya faɗi haka ne bayan wani taron tattaunawa tsakanin ‘yan sanda da shugabannin al’umma a Gombe, inda ya jaddada cewa ingantaccen tsaro yana buƙatar haɗin-gwiwar jama’a da hukumomin tsaro.
Ya bayyana cewa, kodayake jami’an ‘yan sanda na gudanar da bincike kan laifuka da gudunmawar da al’umma ke bayarwa ta hanyar isar da sahihan bayanai suna taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya.
“Idan babu gudunmawar jama’a, ‘yan sanda ba za su iya gano laifuka da kansu ba. Saidai, idan al’umma sun taimaka da bayanai, hakan zai sa hukumomin tsaro su fi samun nasara a aikinsu.”
Kwamared Ubale ya yaba da jajircewar ‘yan sanda wajen kare jama’a, ya na mai cewa fiye da kashi 80 zuwa 90 cikin na jami’an ‘yan sanda mutane ne nagari da ke aiki tare da al’umma domin tsaron lafiyarsu.
Haka nan, ya jinjina wa Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Gombe, CP Yahaya Bello, bisa ƙwazon da ya ke nunawa wajen tabbatar da tsaro.
Ya kuma gode wa Gwamnan Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, bisa irin goyon bayan da ya ke bai wa hukumomin tsaro, ciki har da rarraba sabbin motoci 50 domin bunƙasa ayyukansu.
A cewarsa, wannan mataki na gwamnatin jihar ya taimaka matuƙa wajen sa Gombe ta kasance daya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Najeriya.
Daga ƙarshe, Ubale ya buƙaci al’umma da su fahimci cewa ‘yan sanda na aiki ne domin kare su, ba don cutar da su ba.
“Mu fahimci cewa ‘yan sanda ba abokan gaba ba ne; suna nan ne domin tabbatar da zaman lafiyarmu. Mu cigaba da ba su haɗin-kai domin amfanin al’umma gaba ɗaya”, inji shi.
