Kotu ta taka wa Abba Kabir birki kan rusau a Kano

Daga BASHIR ISAH

Babbar Kotu mai zamanta a Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a S.A. Amobeda, ta dakatar da Gwamnan Jihar, Engr. Abba Kabir Yusuf, daga ci gaba da rushe gine-gine a jihar.

Umarnin Kotun ya biyo bayan ƙarar da wani ɗan Kano mai suna Saminu Muhammad, ya shigar ta hannun lauyansa a gaban Kotun.

Yayin zamanta a ranar Juma’a, Kotun ta bai wa Gwamnatin Jihar Kano umarnin dakatar da ci gaba da rusau a kan wasu gine-gine a yankin hanyar BUK.

Alƙali Amobeda ya ce kada Gwamnatin jihar ta taɓa gine-gine masu lamba 41 da 43 da ke Salanta, a hanyar BUK da ke Kano.

Waɗanda ƙarar ta shafa sun haɗa Atoni Janar na Jihar da Gwamnan Kano da Hukumar Raya Birane ta Kano da Hukumar Kula da Filaye ta Kano da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda da dai sauransu.

Bayan sauraron ƙarar da mai ƙara ya shigar ta hannun lauyansa, Farfesa Nasiru Aliyu, SAN, daga bisani Kotun ta ɗage ci gaba da shari’ar zuwa 10 ga Yuli, 2023.