Kotu ta yi wa Faisal Maina sassaucin zaman gidan yari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kotun Ɗaukaka Ƙara mai zamanta a Abuja ta tabbatar da hukuncin ɗaure Faisal, ɗan tsohon Shugaban Hukumar Fansho da aka rusa, Abdulrasheed Maina bisa laifin haɗa baki da sace kuɗin ƙasa.

A hukuncin da kotun ta yanke a jiya Alhamis, alƙalai uku da suka yi zama sun rage wa’adin da aka ɗiba masa na shekaru 14 zuwa bakwai tun da wannan laifinsa ne na farko. 

Mai shari’a Ugochukwu Anthony Ogakwu da ya jagoranci hukuncin ya bayyana cewa, mai Shari’a Okon Abang na Kotun Tarayya da ke Abuja ya yi gaskiya wajen ɗaure Faisal. Sai dai, inda ya saɓa da Kotun Ɗaukaka aukaka Ƙara, bai yi la’akari da wannan ne laifin Faisal na farko ba, don haka kotun ta rage masa wa’adin da aka ɗiba masa.

EFCC ta gurfanar da Faisal Mana ne bisa aikata laifuka guda uku da suka shafi almundahana da sace kuɗin ƙasa. 

A  ruwaito cewa, Faisal na amfani da wani asusun bogi na bankin UBA, wanda mahaifinsa ya yi amfani da shi wajen zuba kuɗaɗen da suka kai Naira miliyan 58.1, kuma ana zargin mahaifin nasa ya saci kuɗin ne a yayin da yake riƙe da hukumar ta fansho.