Gaskiyar yadda Sajan Rogers ya kashe mahaifiyarmu, inji ’ya’yan Kudirat Abiola

Manhaja logo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Sama da shekaru 26 bayan kisan gillar da aka yi mata, ’ya’yan marigayiya Kudirat Abiola, wadda ta lashe zaɓen shugaban ƙasa da aka soke ranar 12 ga watan Yunin 1993, sun tuhumi Manjo Hamza Al Mustapha, tsohon babban jami’in tsaro (CSO) ga Marigayi Janar Sani Abacha da kitsa kashe mahaifiyarsu.

’Ya’yan marigayiya Kudirat Abiola sun ƙalubalanci Manjo Hamza Al Mustapha su na masu ikirarin cewa mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo ne ya ingiza Sajan Rogers ya sanya sunansa a matsayin wanda ya kashe mahaifiyarsu.

Yaran Kudirat a wata sanarwa da suka fitar kuma suka sanyawa hannu a madadin sauran yaran Khafila Abiola sun bayyana cewa, Al Mustapha ya kashe mahaifiyarsu.

Yaran sun caccaki rahoton da Manjo Al-Mustapha a ciki ya zargi mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo da ingiza Sajan Rogers da yin ƙaryar cewa shi ne ya kashe matar wadda ta lashe zaɓen shugaban ƙasa a ranar 12 ga watan Yunin 1993.

Sun tuno da shari’ar da aka yi a Oputa Panel inda Sajan Rogers ya fito fili ya bayyana cewa shine ya kashe matar tare da yunƙurin kashe Sanata Abraham Adesanya da Cif Alex Ibru, marigayi mawallafin jaridar The Guardian, bisa ga umarnin da Manjo Al-Mustapha ya ba shi.

Sun yi nuni da cewa Al-Mustapha da lauyoyinsa ba su ƙalubalanci shaidar Sajan Rogers a Oputa Panel ba kuma babbar kotun jihar Legas ta yanke hukunci tare da yanke wa jami’an Al-Mustapha da ke ɗauke da makamai zaman gidan yari kan yunƙurin kashe Sanata Adesanya.