
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar Kotun Jihar Kaduna ta yi watsi da buƙatar cire Mai Shari’a Darius Khobo daga cikin masu jagorantar shari’ar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i.
Kotun, a hukuncinta kan buƙatar, ta ce wanda ya shigar da wannan ƙorafi bai janye ‘yancinsa ba na yin ƙorafin zargin ɗaukar ɓangare daga ɗabi’arsa a dokance.
Saidai, Mai Shari’a Khobo ya yi hukuncin cewa matakin bin hanyoyi sama da guda daga mai ƙorafin na shigarwa a gaban Kotun Ɗaukaka Ƙara da Babbar Kotun ta Kaduna, saɓa wa biyayya ga harkokin kotu ne. Haka kuma, mai gabatar da ƙorafin ya gaza bayar da gamsashshiyar hujjar da ke nuna cewa akwai ɗaukar ɓangare akan alƙalin.
Duba da cewa mai ƙorafin ya gaza bada karɓaɓɓiyar hujja akan buƙatar, hakan ya sa kotun ta yi watsi da ƙorafin nasa bisa rashin nagarta. Sannan kotun ta bayar da umarnin a cigaba da shari’ar tsohon gwamna a halin yau da kullum bisa la’akari da yanayin da aka samu kai aciki kuma ya cigaba da zama a hannun Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC).
Daga nan ne ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 12 da 13 ga Oktoba, 2026 don cigaba da zaman da aka saba.
