Kotu za ta tsare Abba Kyari na tsawon kwanaki 14

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A yau Talata ne babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bayyana tsare Abba Kyari da wani mai taimaka masa na tsawon kwanaki 14, bayan da ta amince da buƙatar hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), na neman izinin ci gaba da tsare mataimakin kwamishinan ’yan sandan da aka dakatar, DCP, Abba Kyari da wasu mutane shida, na tsawon kwanaki 14.

Hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi, ta shaida wa kotun cewa, waɗanda ta nemi a ci gaba da tsare su a hannunta, a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike kan zargin da ake musu na safarar miyagun ƙwayoyi.

Darakta mai gabatar da ƙara da shari’a na NDLEA, Joseph Sunday, wanda ya gabatar da buƙatar, ya ce, ana buƙatar wannan umarni ne domin hukumar ta samu damar kammala binciken da ta ke yi da kuma yiyuwar shigar da tuhume-tuhume a kan mutanen da lamarin ya shafa, daga ciki har da na Kyari, da kuma sauran waɗanda ake zargin, Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus.

Bayan ta saurari tuhume-tuhumen d ake yi wa waɗanda ake zargin, Mai shari’a Zainab Abubakar, ta ba da umarnin kamar yadda aka yi nema.

Kotun ta ce, hukumar na da ’yancin neman ƙarin wa’adin, bayan cikar wa’adin kwanaki 14.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *