APC ta miƙa kujerar Shugaban Jam’iyya ga Arewa

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai da takwaransa na Kebbi, Atiku Bagudu su ne suka bayyana hakan ga manema labarai jim kaɗana bayan ganawar da gwamnonin APC suka yi da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ran Talata a Abuja.

El-Rufai ya ce jami’yyar ta amince ta yi rabon muƙaman da babu kowa a kai a tsakanin yankin Arewa da Kudu gabanin babban taronta wanda zai gudana a ranar 26 ga Maris.

Da alama dai jam’iyyar ta ɗauki wannan mataki ne duba da cewa tsoffin shugabannin jam’iyyar, wato John Odigie-Oyegun da kuma Adams Oshiomhole baki ɗayansu ‘yan Kudu ne, don haka ta ga dacewar ɗan Arewa ya shugabanci jam’iyyar a wannan karon.

A cewar El-Rufai, “Mun yarda da tsarin karɓa-karba ga duka shiyyoyi guda shida da ake da su, sannan muka yi musayar muƙamai ta yadda yankunan Arewa za su riƙe muƙaman da ‘yan Kudu suka riƙe a tsakanin shekaru takwas da suka gabata, haka ma ‘yan Kudu su riƙe mukaman da ‘yaan Arewa suka riƙe.

“Don haka wannan tsari ne mai sauƙi kuma a bayyane. Yanzu za mu je mu yi tuntuɓa a shiyyoyinmu sannan mu duba mu ga muƙaman da za a samu, kana shirye-shiryenmu game da babban taronmu za su kankanma nan ba da jimawa ba. Da yardar Allah za mu gudanar da babban taron namu a ranar 26 ga Maris.”

Taron ya samu halartar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo da gwamnonin APC su 19, da suka haɗa da na Yobe, Kano, Kogi, Ekiti, Nasarawa, Kwara, Ebonyi, Jigawa, Lagos, Imo, Ogun, Borno, Niger, Gombe, Osun, Kebbi, Plateau da sauransu.