Kotun Birtaniya na tuhumar Diezani kan zargin cin hanci

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar yaƙi da manyan laifuka a Birtaniya ta tuhumi tsohuwar ministar man fetur ta Nijeriya a kotu, kan laifukan cin hanci.

Ana zargin Diezani Alison-Madueke da karɓar cin hancin miliyoyi barkatai na fam ɗin Ingila daga kwangilolin man fetur da iskar gas, da ta bayar don samun cin hanci.

Ranar 2 ga watan Oktoba, Diezani Madueke za ta bayyana a gaban Kotun Majistare ta Westminster.

Tun bayan kamun da aka yi mata na farko a London cikin watan Oktoban 2015, Diezani Alison-Madueke ta ci gaba da zama a matsayin beli.

Jim kaɗan bayan kama ta, lauyan gidansu ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa za ta yi matuƙar jayayya da zarge-zargen cin hanci da suke bibiyar ta, tun lokacin, da kuma bayan aikin da ta yi a gwamnatin tsohon shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan.

Wata sanarwa da sashen yaƙi da cin hanci da rashawa na duniya a Hukumar Yaƙi da Manyan Laifuka ta Ƙasa ta ce ana zargin Diezani ta ci gajiyar aƙalla fam 100,000 kuxi hannu, da samun zungura-zunguran motocin alfarma da ɗaukar jirgin sama na shata don tafiye-tafiye da tafiya hutun alfarma da kuma kadarori birjik a London.

Shugaban sashen yaƙi da cin hanci na qasashen duniya, Andy Kelly ya ce, “waɗannan tuhume-tuhume, muhimmin abu ne na wani cikakken bincike da sarƙaƙiya a cikin ƙasashen duniya.”

Diezani Alison-Madueke, ‘yar shekara 63, ta kasance a matsayin Shugabar Ƙungiyar ƙasashe Masu Arziqin Man Fetur (OPEC), kuma ministar man fetur ta Nijeriya a tsakanin 2010 zuwa 2015.

Hukumar yaƙi da manyan laifukan ta kuma fitar da bayanai dalla-dalla na ladan kuɗi da ta samu ciki har da kujerun gida da aikin gyaran fuska da ma’aikatan gidaje da ta samu, sannan an yi batun biyan kucin makarantar ‘ya’yanta da kyautuka daga kantuna masu sayar da kayan gayu na alfarma irinsu kantin sarƙoƙin yari na Cartier Jewellery da kayan gayu na kantin Louis Vuitton.

Tuni aka rufe kadarori na miliyoyin fam da ke da alaƙa da laifukan da ake zargi a wani ɓangare na binciken da ake ci gaba da yi, a cewar hukumomi.

A bara ne, hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Nijeriya ta ce ta ƙwace kuɗi sama da dala miliyan 153 da kadarori fiye da 80 daga hannun tsohuwar ministar wadda aka yi imani tana zaune a London.

Ana alaƙanta ta da jerin zarge-zargen halasta kuɗin haram da karɓar cin hanci da batutuwan ƙwace kadarori a Nijeriya da Italiya da kuma Amurka.

Ta yi aiki a matsayin minista daga shekara ta 2010 zuwa 2015, kuma ita ce mace ta farko da ta riƙe muƙamin ministar man fetur a Nijeriya kuma ta farko da ta jagoranci ƙungiyar OPEC ta ƙasashe masu arziƙin man fetur a duniya.

Andy Kelly ya ce: “Muna zargin Diezani Alison-Madueke da tozarta muqaminta a Nijeriya kuma ta karvi ladan kuɗi daga kwangilolin miliyoyi barkatai na fam ɗin Ingila da ta bayar.”

Yayin zantawa da wata jaridar Nijeriya a cikin watan Nuwamban 2015, an ambato ta tana cewa: “Na ƙalubalanci kowa ya kawo hujjar cewa na saci kuɗin gwamnati ko na jama’a.

“Ban tava satar kuɗin Nijeriya ba.”