Kotun Minna ta yanke wa mutane 11 hukuncin kisa ta hanyar rataya

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Babbar Kotu mai lamba 6 dake garin Minna a cikin jihar Neja ta yanke wa waɗansu mutane 11 daga ƙaramar hukumar Lavun hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan ta same su da ɗabagogin laifuka guda tara yayin zaman shari’ar.

Kotun, ta kuma sallami wasu mutanen 15 waɗanda aka gurfanar tare da waɗanda aka yi wa hukuncin kisa, saboda rashin ƙwazo da rashin gurfanar da su bisa tsari ko ƙa’ida.

Waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa sune Mohammed Mohammed, Baba Mohammed, Mohammed Isah, (wanda aka fi sani da Madu), Abubakar Saba, Mohammed Adamu Babamini, Ibrahim Mohammed Emigi, Haruna Mohammed, Isah Baba Madu, Ndama Sheshi, Isah Mohammed da Mohammed Ndabida.

Alqaliyar Babbar Kotun, Mai Shari’a Maimuna Talatu Abubakar ta ce maƙasudin laifin da ya sanya aka yi masu wannan hukunci yana cikin tanadin sashe na 221 (A) ta dokar pinal kod, wanda hukuncin sa kisa ne.

 “Ya kasance wajibin tanadi ne wanda kotun ba ta da wani zaɓi face ta zartar da hukuncin kisa. Na saurari hujjojin lauyoyi. Na yaba wa lauyoyin bisa wahalhalu da suka tunkara, na kuma gaskata da cewar, sun nuna dattaku da halaye na koyi yayin tabka wannan shara’ar.

“Kotun, a wasu halaye ko yanayi makamantan wannan, takan gabatar da shawarwari, amma dangane da wannan laifi da hanyar da aka aikata shi, ba zai kuɓuce ko saki hanya ba.

“Ban kuma yi tunanin samun wata sassauƙar hujja yadda kotu za ta gabatar da shawara ba. Don haka, a bisa laifin farko wanda ya haddasa mutuwar mutane guda bakwai, don haka, na yanke maku hukuncin kisa.

“Na bayar da umarnin kowane daga cikin ku a rataye shi ta wuya har sai ya mutu. Allah ya jiƙan rayukan ku,” inji ta.

Mai Shari’a Maimuna Abubakar sai ta yi furucin, “babban lauyan gwamnati, ta hannun daraktan gabatar da ƙararraki ya gurfanar da ku guda 25 a gaban babbar kotu dake garin Minna a ranar 7 ga Oktoba na shekara ta 2019, bisa laifin kai farmaki wa al’ummar Gaba, dake cikin ƙaramar hukumar Laun bisa batun gonaki.

Babbar Kotun garin Bida, a ranar 22 ga watan Satumba ne na shekarar 2018 ta yanke hukunci da ya daɗaɗa wa al’ummar Gada dangane da rikicin wata gona da al’ummar suka mallaka.

Dangane da laifukan, al’ummar Gaba suna cikin gona, tare da masu safiyo waɗanda suka je domin fitar da iyaka wa gonar, kwatsam sai ga al’ummar Anfani sun kai masu farmaki da muggan makamai, inda nan take aka kashe mutane bakwai.

Mai shara’a Maimuna Talatu Abubakar, yayin da take bibiyar batun, ta yi la’akari da cewar, mai gabatar da ƙara ya gabatar da hujjoji na rashin shakka akan masu laifi, kuma an samu waɗanda aka yi wa hukunci da laifukan su, don haka aka yanke masu hukuncin kisa ta hanyar rataya.”

Ta kuma qara yanke masu hukuncin ɗaurin rai-da-rai bisa wata tuhuma, da kuma ɗaurin shekaru 14 ba tare da zaɓin tara ba, kuma dukkan hukunce-hukuncen za su tafi daura da juna.

Mai Shari’a Maimuna Abubakar ta samu waɗanda aka gurfanar ƙara a gaban kotu da laifukan kisan rayuka a bisa tuhuma ta 9 wanda shi ma yake da hukuncin ɗaurin rai-da-rai, da kuma gamin baki mai hukuncin ɗauri na shekaru 14 ɗabagogi.

Shi dai lauyan kare masu laifi, Barista Lerry Otahagwa tunda farko ya bukaci Alƙalin ta tausaya da yi masu sauƙi yayin yanke hukunci.