Me ya kai Aisha Buhari zauren Majalisar Dattawa?

Daga BASHIR ISAH

Bayanan da suka riski MANHAJA a daidai wannan lokaci na nuni da cewa a karon farko, uwargidan Shugaban Ƙasa Buhari, Aisha Buhari ta ziyarci zauren Majalisar Dattawa.

Ziyarar Aisha ya zuwa zauren Majlisar a yau abu ne mai cike da tarihi, kasancewar wannan shi ne karon farko da irin hakan ya taɓa aukuwa a tarihin Nijeriya inda Majalisar Dattawa ta karɓi baƙuncin matar Shugaban Ƙasa.

Aisha ta halarci majalisar ne don ta shaida miƙa rahoton Kwamitin Majalisar Dattawa kan yi wa Kundin Tsarin Mulki Kwaskwarima.

Majalisar ta jinkirta karɓar rahoton ne musamman don bai wa Aisha damar halartar zaman da za ta karɓi rahoton.

Aisha ta ziyarci Majalisar ne bisa rakiyar Ministar Harkokin Mata, Mrs Pullen Tallen da Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsare, Mrs Zainab Ahmed da sauran hadimanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *