Ku ba mu Naira miliyan 200 cikin kuɗin tallafin fetur – ASUU ga Gwamnatin Tarayya

Daga SANI AHNAD GIWA a Abuja

Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), Farfesa Emmanuel Osedeke ya ce gwamnatin tarayya har yanzu tana nuna halin ko-in-kula akan yajin aikin ASUU wanda hakan ya sa ɗaliban jami’o’in gwamnatin Nijeriya suke zaune a gidajensu.

A cewarsa, gwamnati ta kawo mafita akan kuɗin tallafin man fetur da kasafin Naira tiriliyan 4 amma kuma har yanzu ba ta ce komai ba akan ilimin jami’o’inta.

Farfesa Osodeke ya ce Naira biliyan 200 gwamnati za ta cire daga kuɗin kasafin tallafin man fetur, Naira tiriliyan 4, sannan ta samu rarar Naira tiriliyan 3.8 wurin kawo ƙarshen matsalolin jami’o’i.

Osedeke ya ƙara da kira ga Gwamnatin Tarayya akan nuna muhimmancin ilimi akan tallafin kuɗin man fetur, wanda ya ce shi ne ya fi cancanta a fi darajawa.

A cewarsa, jami’o’in Nijeriya za su iya samar da matatun man fetur cikin shekaru uku, kuma hakan ɗaya ne daga cikin hanyoyin kawo ƙarshen asarorin da ake samu a tallafi.

Farfesa Osedeke ya ci gaba da cewa: “Abin akwai ban mamaki a ce wai gwamnati ba za ta iya tara Naira biliyan 200 duk shekara wurin inganta jami’o’i ba.

“Kuna iya kashe Naira biliyan 228 don ciyar da ɗaliban makarantun firamare da na sakandare. Amma ba za ku iya amfani da kuɗi wurin gyara jami’o’i ba. Wannan ita ce babbar matsala.

“Amma kuma gwamnatin tana iya tara Naira tiriliyan 4 na tallafin man fetur. Tsakanin kuɗin tallafin man fetur da kuma ilimin Nijeriya, wanne ya fi muhimmanci?

“Idan aka cire Naira miliyan 200 cikin Naira tiriliyan 4, don tallafa wa jami’o’i, akwai ragowar Naira tiriliyan 3.8 na kuɗin tallafin man fetur,” in ji shi.