Gwamnatin Tarayya ta bai wa ma’aikatan gwamnatin tarayya wa’adin ranar Litinin, 17 ga Fabrairu, 2025, domin tantance sahihancin bayanansu a shirin kawar da ma’aikatan bogi. A cikin wata sanarwa daga Ofishin Akanta-Janar na Tarayya, an bayyana cewa ma’aikatan gwamnati za su yi rijista ta shafin IPPIS, tare da samar da TIN, lambar IPPIS da lambar asusun albashi.
Sanarwar ta kuma nuna cewa an ƙara wa’adin tantance bayanan albashi har zuwa 17 ga Fabrairu, 2025, domin bai wa waɗanda ba su kammala ba damar yin hakan. Gwamnati ta ja kunne cewa duk ma’aikatan da suka kasa kammala rijistar kafin wa’adin ƙarfe 12 na dare a ranar Litinin, 17 ga Fabrairu, za su fuskanci hukunci da ka iya haɗa da dakatar da albashinsu.
A shekarar 2024, Shugaba Bola Tinubu ya umarci cewa duk ma’aikatan da ke karɓar albashin gwamnati bayan komawa ƙasashen waje su mayar da kuɗaɗen da suka karba. Haka nan, ya bada umarnin hukunta shugabanninsu da suka rufe ido kan wannan badaƙala yayin da suke riƙe da muƙamansu.