Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shuwa-Arab, suna ne na wata ƙabila daga cikin ƙabilun Nijeriya wadda take da asali da Jahar Borno da kuma wasu jahohin Kudu-Maso Yammacin Nijeriya kamar irin su Legas, Oyo da sauran su. Bayan Nijeriya kuma ana samun su a ƙasashe irin su Chadi, Sudan da sauransu. Wikipedia (2020) sun wallafa cewa yawansu ya haura miliyan shida a duniya. Mutane ne su Larabawa, makiyaya, manoma, fitattu wajen kishin Addinin Musulunci da suka bayar da gagarumar gudunmawa wajen kare addinin da kuma tsayar da shi a duk inda suke. Akwai auratayya tsakanin su da Fulani, mutanen da suka yi tarayya da juna ta fuskacin kiwo da kuma yawon neman guri mai ni’ima domin gudanar da sana’ar kiwo da noma.
Suna:
Shuwa-Arab, suna da sunaye mabambanta da ake kiran su da su bisa la’akari da bambancin guri. A ƙasashe irin su Chadi, Kamaru da Sudan ana kiran su da Baggara, wanda kuma jirkitawa ce ta kalmar Larabci wato ‘Baggara’ wadda ke nufin mai kiwon saniya. Wannan kuma saboda zamowar su rabi manoma, rabi kuma makiyaya waɗanda ke samu hanyoyin gudanar da rayuwa ta hanyar kiwo.
Sai kuma a Nijeriya da ake kiran su da suna Shuwa-Arab. Wanda suna ne da aka samar daga kalmomi guda biyu kuma samammu daga harsuna biyu; Kanuri da Larabci aka haɗe su suka zama kalma ɗaya. Kalmar Shuwa, Babarbariyar kalma ce wadda ke da ma’ana ta kyakkyawa ko kuma mai kyau kamar yadda sarkin Shuwa-Arab na Legas ya gaya mana. Ita kuwa kalmar Arab, Balarabiya ce, wadda ake rubuta ta ta da a Larabcen kuma ta ke da ma’ana ta Balarabe. A lokacin da su Baggara suka zo yankin Barno Larabawa ne su farare kuma kyawawa. Saboda haka sai “Kanurai suka riƙa ce da mu Shuwa, Arab; wato Larabawa kyawawa, da haka wannan suna ya bi mu…” inji Sarkin Shuwa Arab na Lagos, Sultan Alhaji Jibril Yahaya.
Asali:
Asalin Shuwa Arab Larabawa ne da suka fito daga yankin Larabawa da ke Gabashi. Jenkins (2006), ya bayyana cewa su, ’yan asalin yankin Hijaz ne; wato Makka da Madina kenan waɗanda daga baya aka haɗe su da sauran yankuna suka zama Saudi Arabia ta yau da kuma sauran yankunan da ke gaɓar Jan Teku.
Sun baro waɗancan yankuna suka kwararo zuwa yamma a cikin ƙarni na goma sha biyu zuwa na goma sha uku (1100 – 1200 CE).
Hijirar su kuwa zuwa wasu ɗaiɗaikun ƙasashe takan bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa. Bethany World Prayer Center (1997), sun ruwaito cewa sun ƙaura zuwa ƙasar Kamaru ne daga Arewacin Afirka ta Tsakiya a matsayin mahara, makiyaya da kuma cinikin bayi.
Hijirar su zuwa Sudan kuwa ta faro daga Yamma zuwa Gabas inda suka tashi daga yankunan Tafkin Chad, gurin da suka daɗe da zuwa daga Arewaci tun zamani mai tsawo da ya shuɗe. Sun yi fice a cikin cinikin bayi a Kudancin Nubiya. Sun baro garuruwansu da ke ƙasar Misira (Egypt) a cikin shekarar 1820 lokacin da shugabannin Daular Othman suke gudanar da shugabancin Kudancin Nubia (Sudan). Haramta cinikin bayi da Turawan Ingila suka yi, shi ne sanadiyar barin su ƙasar biyowa bayan bijirewa Turawan da suka yi ba tare da samun nasara ba, Jenkins (2006).
Braukämper (1996), ya bayyana cewa, Baggara Larabawa ne da suka mamayi yanki mai faɗi a yankin Sabana kamawa daga yankin Farin Kogin Nilu har zuwa Gabashin Barno da ke Jamhuriyar Nijeriya a yau, mamayar da suka yi ta a cikin ƙarni na goma zuwa ƙarni na goma sha uku.
Kakanin Baggara, wato Shuwa-Arab, Larabawa ne makiyaya raƙuma waɗanda suka fara kwarara zuwa Yankin Garuruwan Baƙaƙe (Bilad-Sudan) ta gaɓar Kogin Nilu a cikin ƙarshen ƙarni na goma sha huɗu, inji Braukamper (1996).
Sun ci gaba da kwarara har zuwa tsakiyar ƙarni na goma sha bakwai inda suka kai har yankuna Sahel, gurin da kiwon raƙuma ya gagare su daga baya suka canja sana’a zuwa kiwon shanu da kuma noma, sana’o’in da suka koya daga Fulani da kuma ƙananan ƙabilun guraren da suke zaune, Braukamper (1996).
Daga abin da ya gudana, mai karatu zai iya fahimtar cewa Shuwa-Arab asalinsu Larabawan Saudi Arabia ne, makiyaya raƙuma waɗanda daga baya suka jirkice zuwa kiwon shanu da kuma noma. Sun baro yankinsu na asali suka kwaroro zuwa yankuna garuruwan baƙaƙe, hijirar da suka yi ta daga farkon ƙarni na goma (Kimanin shekaru dubu ɗaya da ɗari ɗaya da shirin kenan da suka gabata; 900 – 2020) har zuwa farkon ƙarni na goma sha tara (1810) a bisa ruwayar Braukamper, (1996); Jenkins, (2006); Bethany World Prayer Center, (1997).
Guraren Zama:
Shuwa-Arab mutane ne da suka fi yawa a ƙasashen Kamaru, Chadi, Sudan da kuma Nijeriya, Bethany World Prayer Center (1997), ƙari a kan waɗannan gurare, ana samun su a ƙasashen Nijar da Afirka ta Tsakiya (Central African Republic), kamar yadda ya zo a ruwayar Jenkins (2006), sai kuma Adeoye (2018), da ya ƙara da cewa ana samun su a Iraƙi da Syria.
A cikin ƙasar Kamaru ana samunsu a mahaɗar Yammacin Kamaru da ta sada ta da Afirka ta Tsakiya (Central Afirka), a cikin dajin Arewa, kusa da Fort-Foureau; yankin da ya haɗa tsakanin ƙasashen Chadi da Nijeriya, abin da yake basu damar kai-komo a tsakanin ƙasashen kodai domin buƙatun yau-da-kullum, ko kuma domin zaman dindindin.
A cikin ƙasar Sudan, ana samun su a Darfur; Kudancin Lardin Kordofan da kuma Arewacin Lardin na Kordofan, Jenkins (2006).
Salon Rayuwa:
Shuwa-Arab, asalin su mutane ne masu rayuwa a daji saboda gudanar da sana’ar su ta kiwo. Sukan tashi daga wannan guri zuwa wancan sau biyu a shekara. A ƙasar Kamaru, sukan tashi daga mazauninsu na dindindin zuwa Kudancin ƙasar inda kogi yake a lokacin rani wanda yawanci yakan faru a cikin watannin Oktoba zuwa Afirilu. Sannan kuma idan ruwan sama ya sauka sai su koma yankin da ke da ciyawa wanda ke Arewacin ƙasar ta Kamaru.
Yawanci suna rayuwa ne da mata biyu a matsugunnan da ke samar da gari a cikin bukkoki. Mace ɗaya takan zauna a gida sannan kuma ɗayar a tafi da ita gurin kiwo da rani. A al’adance, matan ne ke kafa musu bukkoki da kuma ɗakunan da za su zauna a gida da kuma guraren da suke gudanar da kiwo. Namiji, rumfa kawai yake kafawa wadda za ta bashi damar zama da baƙonsa da kuma lura da dabbobi a lokacin da suke kiwo. Bethany World Prayer Center, (1997) da Pray for the Nation, (2005), duk sun ruwaito wannan salon rayuwa na Shuwa-Arab a shafukansu na Intanet.
Za mu cigaba a mako na gaba.