Ku riƙa biyan ‘yan jarida da kyau ko darajar dimukraɗiyya ta zube da labaran bogi – Shugaban INEC ga kafafen labarai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan (SAN), ya yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar darajar dimukraɗiyyar Nijeriya ta rushe muddin aka cigaba da barin labaran bogi da masu ruɗarwa ta fasahar AI suna yaɗuwa acikin al’umma, yana mai cewa wajibi ne masu kafafen yaɗa labarai su fifita walwalar ‘yan jarida a harkar gudanarwa.

Amupitan ya yi wannan gargaɗi ne a ranar Alhamis, 24 ga Satumba, 2026 a taron All Nigeria Editors Conference (ANEC 2026), wanda aka gudanar a Enugu. Da yake jawabi a gaban editoci sama da guda 500, mawallafa da jagororin jarida, Farfesa Amupitan ya bayyana cewa, ba zai yiwu a tsammaci nuna cikakken ƙwarewa ba daga ‘yan jaridar da suke fuskantar barazana ta fuskar tattalin arziƙi yayin sauke nauyin da aka ɗora musu har sai an inganta walwalarsu.

Ya ce, maruwaicin da ke aiki a halin matsin tattali, bin bashin albashi da rashin wadatar walwala, ba zai iya kuɓuta daga karɓar na goro ba daga ɓangaren ‘yan siyasa ko yaɗa labaran bogi acikin al’umma ko kuma jure wa wasu ababen da suka saɓa wa ƙa’idar aikinsa.

Ya shaida wa daraktoci, mawallafa da shugabanni da suka halarci taron cewa walwalar ofishin yaɗa labarai matsalar tsaron ƙasa ce mai zaman kanta, don haka wajibi ne a kula da ita muddin ana tsammanin samun cikakken sakamakon aiki daga ɓangaren ma’aikatan jarida.

Shugaban na INEC ya ƙara da cewa tuni hukumar zaɓe ta ɗauki salon gyara walwalar ma’aikata domin bayar da kariya ga aiki da darajarta a matsayinta na cibiya. Ya ce, hukumar ta samar da sabon tsarin albashi na Consolidated Election Management Body Salary Structure (CEMBSS), wanda ya fara aiki a ranar 1 ga Junairu, 2026, lamarin da ya taimaka wajen daga darajar albashin jami’ansu manya da ƙanana.

Kazalika, shugaban na INEC ya alaƙanta rashin wadatacciyar walwala da taimaka wa yawaitar yaɗuwar labaran bogi da masu ruɗarwa gabanin babban zaɓen 2027. Har illa yau, ya roƙi editoci da su samar da rassan binciken ƙwaf, samar da na’urorin gano bayanan bogi da fifita samar da labarai na gaskiya a madadin rige-rige wajen yaɗawa.

By Babaji

Leave a Reply