Ku riƙe imaninku ko ta halin ƙaƙa – Ƙungiyar Matan Da’awa ga mata

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

An buƙaci mata musamman matan Musulmi da su ke yankin Ƙaramar Hukumar Keffi na Jihar Nasarawa da ma ƙasar baki ɗaya da su ci gaba da riƙe ibada da amanar aurensu a duk inda suka tsinci kansu a kuma kowanna lokaci.

Shugabar ƙungiyar matan musulmi da aka fi sani da ‘Matan Da’awa’ ta ƙasa reshen Jihar Nasarawa, Malama Aisha Ibrahim ce ta yi wannan kira a lokacin da ta ke zantawa da wakilinmu a garin Keffi hedikwatar ƙaramar hukumar Keffi a Jihar Nasarawa.

Ta ƙara da cewa, kiran ya zama wajibi idan aka yi la’akari da matsin tattalin arziki da rayuwar ƙunci da al’umma baki ɗaya musamman mata ke fuskanta a yanzu, wanda a cewarta ya kasance babban ƙalubale da barazana ga imaninsu da ibadarsu da sauran fannonin rayuwarsu baki ɗaya.

Ta ci gaba da bayyana cewa, “shi yasa nake so in yi amfani da damar nan in yi kira musamman zuwa ga ’yan uwa na mata baki ɗaya musamman ’ya’yan ƙungiyarmu ta matan Da’awa a Jihar nan da ƙasa baki ɗaya cewa kada su yarda sheɗan ya yi amfani da waɗannan ƙalubalen rayuwa ya rinjaye su zuwa ga yin wasi da imaninsu da amanar aurensu da sauransu.

“Ina kira a gare su da su cigaba da kiyaye duka dokokin aurensu na sunnah su kuma cigaba da tallafa wa mazajen su da kula da karatun ‘ya’yan su musamman karatun addinin musulunci da na zamani har lokaci da Ubangiji Allah zai kawo sauƙin al’amura.”

Malama Aisha Ibrahim ta kuma yi amfani da damar inda ta yi kira ta musamman ga shugabanni a duka matakai da ma su hannu da shuni cewa su ji tsoron Allah su riqa tallafa wa takwarorin su mata musamman ta tunawa da su a shirye-shiryen gwamnatotin su da samar mu su da jari da bunƙasa fannin lafiyarsu da ilimin su da naɗa su muqaman gwamnati da sauran su don rage musu wahalar ɗawainiyar gidajensu da ta ’ya’yan su da sauransu.

Ta ƙara da cewa sanin kowa ne cewa duk macen da aka tallafawa takan ba da gagarumin gudumawa wajen ci gaban al’umma baki ɗaya a matsayinta na uwa.