Zaɓen Anambara: Dalilin da yasa ba a bayyana cikakken sakamakon zaɓe ba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Duk da cewa an tattaro sakamakon zaɓe a ƙananan hukumomi 19 daga cikin 21 na Jihar Anambra, amma har yanzu ba a bayyana sakamakon ƙarshe na zaɓen ba.

Masu kaɗa ƙuri’a a faɗin Jihar sun fito ƙwansu da ƙwarkwatarsu a ranar Asabar domin zaɓen gwamnansu na nan gaba.

An samu ’yan takara 18 da suka fito neman kujerar a zaɓen, wanda aka dinga samun matsalar na’urar BVAS da aka yi amfani da ita a wasu yankuna.

Sai dai, a wurin karɓar sakamakon na ƙarshe a ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa da ke Awka, Dakta Michael Otu, malami a jami’ar Kalaba wanda ya karɓo sakamakon zaɓe na ƙaramar hukumar Orumba ta arewa, ya ce, ba a yi zaɓe a ƙaramar hukumar ba, inda ya ce, tirsasa shi aka yi ya saka hannu kan sakamakon.

Ya ƙara da cewa, “na matuƙar firgita, idan ba don tsarewar Allah ba, da ban kawo yanzu ba. Na fuskanci mummunan barazana a wannan fitar. Ɗan sanda da aka haɗa mu ya mayar da ni yaron shi. Ko su kallo na suka dinga yi kamar ɗan ta’adda. Har fitsari sai da suka hana ni zuwa. Ban yarda da sakamakon ba, tirsasa ni aka yi na saka hannu.”

Ya zargi Comfort Omoruyi, shugabar zaɓen yankin, da haɗa wannan al’amarin da kanta.

Amma kuma, EO ta caccaki Otu inda ta zargesa da rashin sanin yadda zai sauke nauyin da ke kansa.

Ta ce, shi farfesan shari’a ne, amma kwata-kwata ba shi da hazaƙa kuma bai san komai ba.

Bayan karɓar sakamakon, Obi ta bayyana cewa za a yi taro kan halin da aka shiga a ƙaramar hukumar Orumba ta arewa.

Soludo ne a sahun gaba, APGA ta lashe ƙananan hukumomi 16 a Anambara:

A wani labari kuma daban, akwai manyan alamun da ke nuna cewa jam’iyyar APGA ba ta da niyyar tattara komatsanta ta bar gidan gwamnatin Jihar da ke Awka a Jihar Anambara.

Farfesa Chukwuma Soludo, ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen gwamnan shi ke gaba inda ya lashe zaɓe a ƙananan hukumomi sama da biyu bisa uku na Jihar.