
Daga BELLO A. BABAJI
Cibiyar Bincike kan harkokin noma, IAR ta Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, Jihar Kaduna, ta yi kira ga ƴan Nijeriya da su riƙe tsarin noman masara na TELA a matsayin hanyar magance matsalar yunwa a ƙasar.
Ta ce, hakan zai taimaka wajen tabbatar da tsaro ga samar da abinci da inganta zamantakewa gami da haɓaka tattalin arziƙin ƙasa.
‘TELA maize’ tsari ne da aka samar don inganta nau’ukan ƙwayoyin masara domin magance matsalolin fari da ƙwari masu cutar da amfani gona a yankunan Sahara dake Afirka.
Cibiyar IAR Zaria ta samu sahalewar ƙasa wajen inganta irin noma da suka haɗa da masara, dawa, wake, gyaɗa da makamantansu.
A yayin ganawa da wakilan Blueprint a ofishinsu dake Abuja, Shugaban tawagar cibiyar, Farfesa Licius Bamaiyi, ya bayyana hakan a matsayin matakin inganta abinci da tattali wajen samar da wadataccen abinci ga al’umma da kuma samun ƙarin kuɗin shiga a gare su.
Ya ce, za su yi amfani da fasahar zamani wajen inganta ƙwayoyin amfanin gonar a yayin da suka kaddamar da shirin.
Ya kuma ce, za su tabbatar da aiwatar da shirin wanda ake kira da GMO cikin inganci da kare duk wata cutarwa da ka iya shiga cikin shirin don amfanin ƙasa.
