Kungiyar Hausawa masu sayar da kayan gini a Sabon Gari sun zaɓi sabbin shugabanni

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Kungiyar Hausawa masu sayar da kayan gini na kan titin Faransa a yankin Sabon Gari a ƙaramar Hukumar Fagge su gudanar da zaɓen sabbin shugabannin karo na farko.

An yi zaɓen ne ƙarƙashin shugabancin Alhaji Ibrahim Abdullahi Sani wanda ya ce an yi zaɓe cikin nasara yan takara sun yi abinda ya dace da waɗanda suka yi nasara da waɗanda ba su yi ba an haɗu an tafi cikin fahimtar juna dama a wuri ɗaya ake zaune sannan akwai wayewa a tsakani ba saɓani.

Ibrahim Abdullahi ya ce, dama kafin zaɓen sun tattara masu ruwa da tsaki na zaɓen sun wayar musu dakai akan cewa zaɓe ba ƙarfi ko dabara bane. Allah ne mai bada mulki kuma tunda aka fara zaɓe ba wani abu da aka samu game da ƙorafi ko wani abu na ba daidai ba sannan duk an bi ƙa’idojin zaɓe.

Zaɓen an gudanar da shi ne a gurabe 12 na ’yan takara bisa sanya idanun jami’an ma’aikatar kasuwanci ta jihar kano ƙarƙashin mataimakin Darakta Ibrahim Abubakar Kabara wanda ya tabbatar wa zaɓaɓɓun nasara bayan kammala zaɓen da aka gudanar bisa sa idon jami’an tsaro daban daban da yan jarida.

Isah Umar ne ya sami nasarar zama zaɓaɓɓen shugaban ƙungiyar da ƙuri’u 192 daga cikin waɗanda suka yi nasara akwai Kamalu Aliyu Jami’in hulɗa da jama’a da ƙuri’u 199. Mataimakin jami’in walwala Abdullahi Sulaiman 236. Sakataren Kuɗi Kamilu Abubakar 172.Mataimakin sakataren ƙungiya Khalpha Awwal 326, Sakatare Kamal Sharif 169, jami’in walwala Aliyu Manta 181, da sauran waɗanda suka yi nasara.

Sabon shugaban ƙungiyar Isah Umar a jawabinsa bayan tabbatar masa da samun nasara ya godewa Allah da al’umma da suka zaɓe su da roƙon Allah ya basu kwarin gwiwa domin tabbatar abinda suka alƙarwanta ’yan ƙungiyar lokacin neman zaɓe.

Ya yi nuni da cewa akwai abubuwa na ƙalubale  da masu sana’ar kayan gini suke fuskanta shine yasa ma suka shiga zaɓen mafi muhimmanci shine yanda kasuwancinsu ke yin baya kuma akwai abubuwa da yakamata su haɗu don ciyar da kasuwar gaba amma saboda babu tsayayyen shugabanci basu sami wannan damar ba amma yanzu sun ɗaura ɗamara akan waɗannan abubuwa da yardar Allah kuma za suyi nasara.

Sabon shugaban Isah Umar ya ce in Allah yaso ƙungiyar zata zauna da ƙafarta da samar mata ofis don gudanar da ayyuka kuma duk shekara zasu fito su yiwa mutane bayani akan  irin nasarori da suka cimma da yardar Allah. Ya ja hankalin waɗanda suka shiga zaɓe basu kai ga yin nasara ba su zo a haɗu domin cigaban harkokinsu na kasuwanci.

By ukarofi