Kwalejin fasaha ta tarayya ta Ƙaura Namoda ta yaye ɗalibai 1,450

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya da ke Ƙaura Namoda a Jihar Zamfara ta yaye ɗalibai 1,450 da aka ɗauka da za su karanci Diploma ta ƙasa da babbar diploma ta ƙasa daban-daban don zaman karatu na shekarar 2025/2026.

Shugaban kwalejin Dr. Aminu Yusuf ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyi ga manema labarai a ƙarshen bikin kammala.

An gudanar da bikin a babbar harabar kwalejin da ke garin Ƙaura Namoda, hedikwatar ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda a yau Juma’a.

Ya jaddada cewa wasu daga cikin nasarorin da aka samu a ƙarƙashin jagorancinsa sun haɗa da, kammala katanga mai tsawo kilomita 2.5 a kwalejin don inganta tsaro, Kammala sashen abinci mai gina jiki da kuma kammala cibiyar ICT da ya kai kashi 80%.

Ya yaba wa hukumar ilimin fasaha ta ƙasa (NBTE) saboda amincewa da kwasa kwasai 38 a cikin shekara ɗaya da ya yi a ofis.

Ya kuma yaba da ƙoƙarin gwamnatin jihar Zamfara da ta gina masaukin ɗalibai na zamani ga ɗaliban kwalejin.

Dakta Yusuf ya ƙara yaba wa ƙoƙarin Hon Abdulmalik Zubairu, ɗan majalisar wakilai, mai wakiltar mazabar Bungudu da Maru, wanda ya samar da rijiyoyin burtsatse guda biyar masu injin don amfanin ɗaliban kwalejin.

Shugaban kwalejin ya yaba wa gwamnatin jihar Zamfara da NBTE saboda goyon bayan da suka bai wa kwalejin.

Ya yi kira ga sabbin ɗaliban da suka shiga kwalejin da su kasance masu bin doka da oda kuma su guji munanan halaye da ka iya ɓata sunan kwalejin.

By ukarofi