Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau
Kwamishinan Harkokin Addini na Jihar Zamfara kuma babban limamin masallacin Juma’a na Muslim Foundation da ke Gusau, Dr. Sheik Tukur Sani Jangebe ya yi murabus daga muƙaminsa.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 1 ga Mayu, 2022 wacce ya sanya wa hannu kuma Blueprint Manhaja ta mallaki kwafi ranar Litinin a Gusau.
Sheik Jangebe ya miƙa godiyarsa ga Gwamna Bello Mohammed Matawalle bisa damar da aka ba shi na zama ɗaya daga cikin mambobin majalisar zartarwar jihar na tsawon shekaru uku.
Sai dai, Dr. Sheik Tukur Sani Jangebe bai bayyana dalilin ajiye aikinsa na kwamishinan gwamnan jihar Zamfara ba a wasiƙar.
“Mai girma gwamna ina mai sanar da kai cewar, ni Dr. Sheik Tukur Sani Jangebe na miƙa takardar ajiye aikina a matsayin Hon. Kwamishinan Harkokin Addini a yau 1 ga Mayu, 2022,” a cewar wasiƙar.
Baya ga godiaa da ya nuna, Sheik Tukur Sani Jangebe ya yi alƙawarin ci gaba da bai wa gwamnatin jihar Zamfara dukkanin goyon bayan da ya kamata a ƙarƙashin jagorancin gwamna Bello Mohammed Matawalle domin samun nasara.
“Ina miƙa godiyata ga Gwamna Bello Mohammed Matawalle bisa damar da aka ba ni a matsayina na kwamishina kuma memba a majalisar zartarwa ta jiha kuma zan ci gaba da yi wa gwamnatinku addu’ar samun nasara,” inji shi.
