Daga SANI AHMAD GIWA
Hukumar Tace Finafinai da Bidiyo ta Ƙasa, NFVCB, ta ce, hukumar ta karɓa tare da tace finafinai 541 da masana’antar finafinan Nijeriya ta Nollywood ta shirya a farkon kwata ta shekarar 2022.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Adedayo Thomas, Babban Daraktan NFVCB ya fitar a Juma’ar makon jiya a Abuja.
Ya ce sashen Tace Finafinai da Tantancewa na hukumar ne suka fitar da wannan ƙididdiga a cikin rahotonta na kwata ta farko na shekarar bana.
Thomas ya ce, rahoton ya ɗauki dukkan finafinan da aka miƙa wa hukumar daga sassan ƙasar.
Ya ce za a gabatar da rahoton ga hukumomin Gwamnatin Tarayya da abin ya shafa don tattara abubuwan da aka samar na cikin gida, GDP, na kashi na farko na GDP, Q1, 2022.
M. Thomas ya qara da cewa rahoton kwata na farko ya nuna cewa an samu ƙaruwar finafinan da aka yi daga 382 a kwata na ƙarshe na shekarar 2021 zuwa 541, wanda ke nuna ƙaruwar kashi 42 cikin ɗari.
“Mun yi farin ciki da cewa masana’antar ta fara wannan shekara a bisa kyakykyawan tsari kamar yadda aka nuna a cikin ƙaruwar adadin finafinan da hukumar ta samu don tantancewa da amincewa a cikin kwata na farko.
“Ko shakka babu masana’antarmu ta fim ita ce babbar hanyar da za ta taimaka wa tattalin arzikin ƙasa, kasancewar finafinan da ake shiryawa na nuni da irin ayyukan yi kaitsaye da kuma kaitsaye da sashen ke samarwa,” in ji Thomas.