Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinan Hausa ta Nijeriya, wato Motion Pictures Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN), reshen Jihar Kano, ta gabatar da taron shan ruwan azumi da kuma ƙaddamar da sabbin shugabanni na Jihar Kano da ya gudana a Kannywood TV a Kano.
A jawabinsa, Farfesa Abdullahi Uba Adamu, wanda shine baƙo na musamman a wurin, ya ce, a ra’ayinsa da ma babu wanda ya fi cancanta da ya riƙi shugabancin Kannywood, kamar Ado Ahmad Gidan Dabino, yana mai cewa, wannan ne dalilin da ya sa ya ba shi wani kundi, wanda idan ya bi shi, zai iya warware matsalolin masana’antar.
“Domin shine kaɗai ya fi kowane jarumi samun kyaututtuka a Kannywood, ana maganar sarki a Kannywood, to mu gwamna muke da shi a Kannywood kuma kowa ya san gwamna gaba ya ke da sarki,” inji Farfesa Abdalla.
Sannan ya bai wa sabon shugaban kundin manhaja na tsarin yadda ya kamata a gudanar da fim ɗin Hausa da British Council ta bayar tun a shekarar 2003, wanda ya ke ɗauke da yadda za a tace a kuma tsarkake Finafinan Hausa, ya ce, kundin yana ƙunshe da bayani dalla-dalla akan matsalar Finafinan Hausa da kuma yadda za a warware matsalar Finafinan Hausa.
An dai zaɓi Malam Ado Ahmad Gidan Dabino (MON) a matsayin Shugaba da mataimakinsa Garba Sunusi Kalambaina da Kamal S. Alƙali a matsayin Sakatare da Mataimakin Sakatare Balarabe Murtala Baharu da Ma’aji Sulaiman Abubakar da Sakataren Tsare-tsare Nura Sharif, sai Mai Binciken Kuɗi Hayatudden Yakubu da Jami’ar Walwala Asma’u Sani da Jami’in Yaɗa Labarai I Misbahu M. Ahmad da Jami’in Yaɗa Labarai II Mubarak Abba da Sakataren Kuɗi Isma’il Khalil Ja’en da sauransu.
Tun da farko a jawabinsa, Sheikh Yahaya Maimota ya gabatar da nasiha mai taken ‘Muhimmancin Neman Ilimi’, ya ce, “wanda duk ya ji tsoron Allah akan ko mene ne, to Allah zai ba shi mafita a rayuwa, sannan kuma Allah zai azurta shi ta inda ba ya zato.”
Sheikh Maimota ya ƙara da cewa, “Don haka a rayuwa duk abinda za ka yi ko mene ne za ka yi, to ya zamana ka na tafiya da tsoron Allah a ciki, sai ka ga Allah ya sanya albarka a cikin lamarin.”
Sannan ya qara da kira ga sababbin shugabannin da aka zaɓa da su ji tsoron Allah kuma su yi aiki tuƙuru, don ganin sun ciyar da ƙungiyar MOPPAN gaba.