Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban kwamitin Alhaji Khalil Baƙo ya faɗi haka a hira da manema labarai a Katsina.
Ya ce dole ne a ƙwace filayen a dazukan da ke mallakan gwamnatin Jihar Katsina da aka mallaka ba bisa ƙa’ida ba, a maida wa gwamnati.
A cewarsa ,an sami rahoton wasu mutane suna bayar da filayen dazukan gwamnati ba bisa ƙa’ida ba inda yayi gargaɗi duk wanda aka kama da aikata wannan ɓarna zai fuskanci shari’a.
“Haƙƙin gwamnati ne ta bayar da filayen ga waɗanda suka cancanta da tabbatar da anyi amfani da su ta hanyoyin da suka dace”inji Khalil.
Ya ja hankalin jama’a da su guji amfani da filayen dajin na gwamnati ba tare da sahalewar hukuma ba,domin kaucewa shiga matsala.
Kwamiti ya ziyarci dajin Daban gwamna,dajin Sonkaya da dajin Atakar a ƙananan hukumomn Mai’adua da Mashi da kuma dajin Makau a ƙaramar hukumar Bindawa da sauran wasu dazuka da ke faɗin jihar.
Yan kwamitin sun haɗa da shugaban ƙaramar hukumar Katsina Hon Aminu Ashiru kofar Bai da Ɗan Iya Daura hakimin Ɓaure da wakilan kwamishinan ‘yan sanda da jami’an tsaro na farin kaya da ma’aikatan muhalli.
