‘
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hukumar ‘yan sanda a Katsina na binciken yadda wani ɗan sintiri ya harbi Sa’idu Abdulkadir ɗalibi a jami’ar gwamnatin tarayya da ke garin Dutsinma a Jihar Katsina.
A wata takardar sanarwar ɗauke da sa hannun jami’in yaɗa labarai na ‘yan sanda DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar da afkuwar lamarin.
Ya bayyana cewa binciken da suka gudanar ya nuna cewa wani mai mashin na haya ɗauke da wannan ɗalibi sunci karo da motar su ƙirar Hilux “nan take ɗaya daga cikin ‘yan sintiri ya kai masu harbi”inji DSP Aliyu.
“Bayan samun labarin haka jami’an mu suka isa wurin inda nan take suka ɗauki shi wannan ɗalibi zuwa asibitin Dutsinma daga nan suka wuce da shi zuwa asibitin ƙashi a Katsina inda ya rasu”DSP Aliyu ya ce.
DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce hukumar ‘yan sanda a Katsina ta damu ƙwarai da afkuwar lamarin kuma ta duƙufa wajen gano ɗan sintiri da yayi harbin.
A halin da ake ciki yanzu haka ɗaliban jami’ar na nan na gudanar da zanga-zanga kan kisan Sa’idu Abdulkadir wanda yana cikin shekarar ƙarshe na kammala karatun sa a jami’ar.
