Kwaroroton ƙarya da Salihu Mohammed yake yi

Daga INJINIYA SANI USMAN KABIRU

Daga farkawa ta da safe na ci karo da wani rubutu mai matuƙar ɗaga hankali mai taken ” Ɓaraka a shugabancin APC na ƙasa domin Adamu yana cikin gararin saboda sabon salon shugabanci”. Da fari ban yi niyyar cewa komai ba a game da wannan rubutu ba. Amma kuma sai na ga ya dace na kare matsayinsa na mai ruwa da tsaki a cikin jam’iyyar.

A cikin wannan rubutu dai, mataimakin shugaban jam’iyya na yankin Arewa maso Yammacin qasar nan, Salihu Mohammed Lukman, ya ce ya aike da wani jawabi da aka sanya wa kwanan watan 22 ga watan Mayu, 2022, kuma aka aike da saƙo shugaba jam’iyyar APC, Abdullahi Adamu, mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, mai taken “Sabunta APC: buƙatar samar da sabbin tsare-tsare.” Sannan ya yi mashiriricin ikirarinsa na buƙatar a kauce wa kura-kurai baya wajen gudanar da jam’iyyar APC.

Salihu ya yi ikirarin cewa, sabon shugabancin APC na ƙasa a ƙarƙashin Adamu yana koyi da salon mulkin tsohon shugabancin Adams Oshiomole da Mai Mala Buni, inda za a tattauna a kan ayyuka, amma ba a tabbatar da su. Sannan kuma mambobin jam’iyyar an yi shakulatin ɓangaro da su ba a tafiya tare da su.

Sannan wani sashen wasiƙar ya ƙara da cewa, har yanzu dai ba ta canza zani ba a wannan sabon shugabanci domin har yau ana yanke hukunci cikin nuƙu-nuƙu ba tare da an bayyana shi ga mamabobin jam’iyyar ba.

Har ma ya bayyana cewa, “Har yau an kasa tantance ‘yan takarar shugabancin ƙasar nan a ƙarƙashin APC. Kuma hujjar da aka bayar wai har yanzu ana jira ne a tuntuɓi shugaba Muhammadu Buhari. Wanda hakan rashin adalci ne ga shugaban ƙasar. Domin wani salo ne na fakewa da shi don a kare matsalar da aka samar”.

Amma sam ba haka al’amarin yake ba, domin tarurrukan ganawa na Shugabancin ƙasa na APC ana yin sa kusan kowanne mako. Kuma Mambobin jam’iyyar suna halarta kan jiki,kan ƙarfi. Kuma suna ba da gudunmowoyi sannan su yi suka a inda ya kamata.

Domin abin arziki ne ma a ce kana tare da Mambobi ko da kuwa kuna samun saɓani ne. Kuma wannan tabbas ya yi hannun riga da mulkin baya da aka ce Adamu yana bi sau da ƙafa. Inda shugaban jam’iyya na ƙasa zai gudanar da taro kuma ya qi ba wa Mambobi dama kataɓus.

Kuma babban ƙalubalen da aka ce ana fuskantar cewar hukuncin da aka yanke ba a tabbatarwa. Amma matsalar da shugabancin baya na Adams Oshiomhole da Mai Mala Buni suka fuskanta na rashin tabbatar da abubuwa ba ya rasa nasaba da rikicin shugabanci da ya addabi jam’iyyar a wancan lokacin.

Na shafe fiye da shekaru 40 ina gwagwarmayar siyasa amma ban taɓa karanta rubutu mai cike da son rai da rashin tunani ga ɗan siyasa kamar wannan wasiƙa ba. Salihu da ma can mutum ne mai karaɗin tsiya. Na faɗi haka ne saboda na san shi da kyau. Duk lokacin da wani abu ya faru, shi ne mutum na farko da zai fara karaɗi. Kuma duk wani abu na son zuciya idan ya gifta, Salihu shi ne kan gaba. Ba abin mamaki ba ne don ya kasance mutum na farko wajen neman abinda ya nema a cikin wasiƙar.

Na ji daɗi matuƙa sosai a lokacin da sabon kwamitin na APC ya duba wannan bayani na vatancin da Salihu ya yi cikin damuwa ya kira Shugabancin APC na ƙasa domin su kore wannan wasiƙa ta tawaye da neman gindin zama domin Salihu ya riga ya zame wa jam’iyyar ƙarfen ƙafa wanda zai jawo mata baƙin jini.
Sam ba adalci yadda a cikin watanni biyu kawai da ƙaddamar da shugabancin jam’iyyar sannan da gabatowar zaɓen 2023 yadda INEC ta tsara shi a tsuttsuke a ce Salihu ya takali Shugaban jam’iyyar a kan abubuwan da suka shafi sha’anin ma’aikatunsa da hikima (ta mulki). Wannan ƙarara ya nuna rashin dacewar Salihu a wajen aiki da tsararriyar ƙungiya mai tsararren shugabanci.

Sanata Abdullahi Adamu shugaba ne na ƙwarai. Kuma ba abin mamaki ba ne cewa miliyoyin masu biyayya ga jam’iyya sun yarda cewa yana da dukkan nagartar kamar dattaku da gogewa na shugabantar jam’iyyar musamman wannan lokaci na zaɓe.

A yanzu haka APC ta samu mutumin da zai ceto ta don kai ta zuwa gaci irin na siyasa, jam’iyyar a halin yanzu tana cikin hannayen da aka gwada kuma aka ga nagartarsu da amanarsu. Jam’iyyar ta samu madugu uban tafiya da kuma shugabanci nagari. Bugu da ƙari, jam’iyyar ta samu cigaba, kuma babu wanda zai iya hakan a kaf APC sai Sanata Abdullahi Adamu kuma ga shi yana yi ɗin.

A wannan gaɓar ne kuma zan yi kira ga Salihu Lukman da ya jingina kwaɗayinsa na siyasa a gefe guda, ya gode Allah da ya ba shi mutumin da zai zamar masa malami wanda zai masa jagora a mahangar siyasarsa da turbr muqaman siyasa. Ruwa cikin cokali ɗaya dai ya ishi mai hankali wanka.

Injiniya Kabiru ya rubuto ne daga Abuja, kuma za a iya samun sa a [email protected]