Tattaunawa da Shugaban Ƙungiyar Manoma Alkama, Alhaji Salim Sale Muhammad

Noman alkama noma ne wanda a baya a ƙasar Nijeriya ba ta kasance cikin ƙasashen da suka samu cigaba a fannin B ba. Amma ya zuwa yanzu ƙasar nan tana kan gaba wajen nomawa da sarrafa alkama a Afrika. Don haka ne ma, wakilin Blueprint Manhaja, Babangida S. Gora ya samu zantawar da shugaban ƙungiyar manoma alkama ta ƙasa, Alhaji Salim Sale Muhammad, kuma ga yadda hirar ta kasance. 

MANHAJA: Da farko za mu so mu san da wa muke tare a halin yanzu?
ALHAJI SALIM: A’uzubillahi minashaiɗanir rajim bissimillahirrahamanir Rahiim, Sunana Salim Saleh Muhammad, shugaban Manoma Alkama na Nijeriya.

Da farko za mu so ka gaya mana shi kansa noman alkama ya yake? 
To Alhamdullahi, kamar dai yadda kowa ya san menene noma, wanda har Hausawa na yi masa kirari da “na duƙe tsohon ciniki, duk wanda ya zo Duniya kai ya tarar”. Sannan kuma ita dai alkama wani nau’ine na abinci da yawanci ƙasashen gabacin Duniya da kuma Larabawa sukafi amfani da ita. Wato ƙwaya ce kamar sauran ƙwayar gero, dawa, masara da sauransu. Amma kuma tana da sidarin gina jiki mai tarin yawa da ya ɗara na sauran ƙwayoyin abinci. Haka kuma ita ce nau’in abinci da ta fi karɓuwa a sauran ƙasashen Asiya da ƙasashen Larabawa. Daga bisani kuma a nan Afirika muka samu irin ta Afrika kuma a Najeriya.

Ko ƙasar Nijeriya tana kan gaba wajen samar da alkama?
To ba zan ce ƙasar Najeriya tana kan gaba ba wajen samar da alkama, idan ka dubi taswirar Duniya. Amma a Afirika ta Yamma, za mu iya yin alfahari wajen taka rawar gani sosai, kuma Nijeriya tana kan gaba wajen alhafari da sauran ƙasashen dake nomata suke yi, da ake kallonta a Duniya a matsayin matattara ta sayar da alkama. Domin ba mu mai da hankali wajen nomanta ba, kasancewar duk matakai da za a ɗauko wajen noman ta sai su kare. Don ana sa siyasa a cikin tafiyar. Kamar yadda muka samu labari, akwai cinikayya da Amirka tana sayan ma nfetur daga Nijeriya ita kuma tana sayen alkama ta hanyar ‘ban gishiri in ba ka manda’. Don haka, sun lura manoman Nijeriya suna da basirar duk abinda za ka koyar da su cikin ƙanƙanin lokaci za su fahimce shi har ma ka ga suna neman fin wanda ya koyar da su abin kaifin basira. Don haka, suka bijiro mana da siyasa iri-iri.

Waɗanne hanyoyi kuka bi don gargaɗi da harkar noman alkama a tsahon shekaru huɗu da ka kwashe kana shugabantar manoma alkama?
Kafin mu zo kan wannan kujera, akwai shiri a kan noman alkama da aka yi guda biyu, lokacin tsohon shugaban ƙasa na zamanin soja. Watau Janar Ibrahim Babangida ashekara ta 1983. Sai kuma lokacin tsohon gwamnan babban banki akunyumi, amma daga zuwa na a yanzu mun yi tunanin hanyar da ta kamata mubi dan maido da martabar noman alkama awannan ƙasa, dan haka muka fara qulla yarjejeniya tsakaninmu da sauran ƙungiyoyi na duniya da suke tallafa wa noma a Duniya. cikin haka ne ma muka ci karo da Sir SC project da suka tallafa mana matuƙa wajen kawo canji a wannan tafiya tamu. Sannan sun kawo mana hanyoyin da za mu inganta wannan noma ta hanyar zamani. Bayan haka kuma, sun taimaka mana wajen samun ilimin noman alkama daban-daban, tare da samar mana da na’u’in irin alkama yakai kala biyar zuwa shida a ƙasar nan, wanda da irin da muke da shi shi ne, kilaki da ake yi a yankin Haɗejia ta Jihar Jigawa.

Yaya batun tasgaro ko matsalolin da kuke fuskanta?
Kusan sanda muka yunƙuro kuma kan batun noman alkama da samun cigaba sai kuma aka fara magana kan batun alkamar Nijeriya tana da tarkace kuma gajerar ƙwaya ce ba ta da tsayi. Sannan sun ƙalubalanci alkamar Nijeriya ba za ta shiga injinansu ba  saboda ba ta da tsayi. Kuma sun ce alkamar Nijeriya ba za ta iya yin burodi ba da dai sauran ire-iren waɗannan maganganun. To mu da muka zo, sai muka ɗauki wannan a matsayin ƙalubale. A zuwan mu kuma kasancewar muna da masana sosai, kuma muka samu wani kamfani mai suna “Pure” muka zauna da su. Inda suka buƙaci mu kawo samfurin alkamar tamu don sata a ɗakin gwaji tare da gwadawa don gano gaskiyar yadda take. Sai ga shi an yi burodi da ita, ya yi kuma kamar tasu ta wajen. Daga nan kuma suka ƙara sukar alkamarmu ta cewa ba ta da kyau. Idan ka saui buhu guda, to da kyar za ka samu rabin buhu a cikinta. Nan take sai muka ɗauki wannan ƙalubale tare da neman gwamnati ta tsaya mana. Inda muka karɓi bashin Naira miliyan ashirin a Bankin Union Bank. Inda muka sayo injinan zamani da za su iya fidda dogayen  kwaya da gajeru kuma ta rinƙa fita fes. Saboda idan manomi ya kawa mana muka gyara muka sa a buhu, sai ka ce ta zo daga rasha ko Amurka. Wannan ma siraɗin ma muka tsallake. Bayan wannan kuma, sun zo da maganar cewa, alkamar Nijeriya ba ta da sinadarin gulotamin da yake taimaka wa burodi ya tashi tare da sarrafa ta zuwa wasu nau’in abincin. A nan kuma sai aka zo da batun cewa ai yawan cin gulotamin yana kawo cutar makanta da sauran wasu cututtuka. Don haka aka ce ai alkamar Nijeriya ba ta da yawan gulotamin, don haka, za su cigaba da sayenta. Kuma wannan shi ne ya ba mu ƙwarin gwuiwa wajen cigaba da shugabantar wannan tafiya. Dan haka kamfanoni da dama, sun nuna sha’awar haɗa hannu da mu. Inda kamfanin sarrafa alkama zuwa taliyar yara watau indomie ya fara magana da mu. Inda muka noma masu alkama sukai amfamin da ita. Daga nan kuma muka shiga ƙulla yarjejeniya tsakanin kamfanonin fulawa muka ce kuzo mu rinƙa noma muku alkama kuna biyan mu. Nan muka ƙulla yarjejeniyar shekaru biyu. Kuma ita ce har yanzu dat a ɗore. Bayan mun ga kasuwar ta buɗe, shi ne bana muka ce bari mu je mu karɓi bashi. Inda bana muka noma hekta dubu sittin. Inda yanzu haka girbi muke muna biyan bashin da aka ba mu.

Shin ko akwai wasu hanyoyi da gwamnatin Tarayya take tallafa muku?
Gaskiyane ita gwamnati Muhammadu Buhari ta sahale wa babban bankin ƙasa na CBN da ya shigo mana da ingantaccen irin alkama, kuma sun kawo, sun ba mu, an shuka; an kuma ga alfanunsa. Sai shi kansa tsarin noman ɗangata da ake yi na anchor borrowers da gwamnatin Tarayya ke yi. ba a fara kan kowa ba bana sai kan manoma alkama. Inda za ka noma alkamar bayan an baka kayan noman da duk kake buƙata. sannan idan ka yi noman ma za ka mai da bashin da ka karɓa ta hanyar abinda ka noma. Idan ma ka rage kayan, ba za a bar ka ka je kasuwa da shi ba. Nan take za su saye sauran kayan da ya rage maka. Da ƙalubale a cikin noman alkama, amma alhamdullahi ƙalubalen sai ya zamar mana ilimi ne da kuma fahimtar hanyar ƙara bunƙasa wannan noma.

Batun nasarori kuma fa?
Alhamdullahi, nasara ta farko ita ce, matsayina na shugaba, yanzu haka alkamar Nijeriya  ta samu karɓuwa kuma an yarda zaa iya amfani da ita ga kowane nau’in abinci kuma ta ba da abinda ake so. Sai nasara ta biyu ita ce, a baya ba mu da manoman alkama a ƙasar nan, amma kuma yanzu haka muna da jahohi 19 da mutanenmu suke noma alkama. Bana mun yi amfani da sha huɗu, kuma shekara mai zuwa za mu sa sauran. Sannan kowace jaha muna da wakilci na shugabanni.  Batu na uku kuma shi ne, yadda gwamnati ta yarda mu ne manoman alkama. Ta kuma ba mu bashi don mu yi wannan noma. Sai kuma akwai dabaru da ilimin noman alkama da jama’armu suke samu don zamanantar da noman. Babbar nasarar a nan ita ce, manomi zai noman bai asara ba, zai ci riba tare da ciyar da iyalinsa.

Bayan noman ɗangata da tallafin Anchor Borrowers, wanne ƙarin yunƙuri gwamnati ta taɓa yi muku?
Banda wancan batu na anchor borrowers akwai African Development Bank da yanzu haka zai sa hannun jari a ƙarƙashin shugabancina na shugaban manoma alkama na ƙasa. Inda za a noma hekta kimanin dubu ɗari biyu da hamsin, don a ciyar da ƙasarmu da kuma sayar wa a kasuwanin Duniya. Sannan yanzu haka kuma, akwai ƙungiyoyin ƙasashen Duniya da suke buƙatar haɗaka da mu don samun alkama daga Nijeriya duk da cewa tsari ne mai girma zuwa nan gaba. Amma dai ka ga waɗannan  nasarori ne da za mu iya cewa, ana samu. Akwai ƙasashe biyu dake kan gaba wajen samar da alkama wato, Rasha da Yukiren. Kana ganin takun saƙar dake tsakaninsu zai iya kawo tsaiko a samunta a Duniya bakicaya.
Eh, za mu iya kallon abun ta siga biyu. Na farko, zai iya zama koma-baya ta fuskar yaƙin da suke yi ta ya tava tattalin arzikin ƙasashen Duniya ta nau’in abinci da cinikayya, da zaman lafiya. Mu ma nan ya shafe mu wajen sayen alkama. Don muna sayen kaso talatin cikin ɗari daga waɗannan ƙasashe. Siga ta biyu kuma, wata dama ce ga Nijeriya don bunƙasa noman alkama don ci da ƙasar nan da kuma bunƙasar tattalin arzikinmu. Idan gwamnati ta miƙe ta yi hoɓɓasa wajen cike wancan givin da aka rasa, dan bunkasa tattalin arzikin qasa da samun kuɗaɗen shiga tare da rage zaman banza dake jefa matasanmu a harkokin garkuwa da mutane da sauran matsaloli da daman gaske. Haka kuma idan ka fidda kamfanoni dake sarrafa ta zuwa abubuwa daban-daban. Idan ka dawo cikin gida, mata mu suna amfanin da ita tun daga batun sarrafa ta zuwa abinci kala-kala kamar burabusko, tuwon alkama da dai sauran abinci nau’ika da dama. Sannan kuma alkama ta fi sauran abinci da muke amfani da su alfanu.

Alkamar da ake nomawa a Nijeriya za ta iya wadata ƙasar?
Alkamar da muke nomawa a nan ƙasar ba za ta iya wadatar da ƙasarmu ba. Ɗan abinda muke buƙata ya wadatar da ƙasarmu shi ne tan Miliyan biyar da dubu ɗari biyu. Mu kuma abinda muke nomawa ko rabin miliyan ba mu yi ba. Ka ga abin yana da yawan gaske, amma a yanzu da muka mai da hankali a kan wannan noma da muke yi da wanda muke sa ran za mu yi, za mu iya samun kaso ashiri zuwa ashirin da biyar cikin ɗari insha Allahu.

A da jihohin Arewa da dama ba sa noma alkama. Ya abin yake a halin yanzu?
Wannan haka yake a cikin jihohi sha tara da muke da su a Arewacin ƙasar nan. Amma Arewacin Arewa ko’ina suna noma alkama. Kama daga Jihar Jigawa, Kano, Kebbi, Katsina, Zamfara da jahar Sokoto da Kaduna. Amma zuwanmu muka ce to su sauran jihohin kuma na Arewa fa? Nan take muka sa aka yi mana bincike shi ne muka sa Jihar Bauchi, Filato, Gombe, Adamawa, Taraba da jihar Barno da ma Jihar Neja, Minna kenan. Ka ga ba za mu iya noman alkama gabaɗaya jahohin Nijeriya ba, don kuwa alkama tana yi ne a lokacin hunturu, watau lokacin sanyi. Kuma ka ga ba ko’ina a jihohin Nijeriya ke da wanna yanayi ba, sai waɗannan gurare. Saboda haka, idan noma a wacannan gurare ya bunƙasa. Sai masana suka gano mana. Yanzu haka akwai nau’in alkamar da zai iya yi da damina da za ta iya yi a jihohin Jos, Mambila da Ubudu. Don haka, tashin farko a bara sai muka gwada shi a Jos. Daga baya muka ce, me zai sa ba za mu gwada shi a Arewacin Arewar ba? Shi ne muka ɗauki Bauchi, Kano, Sokoto, Birnin Kebbi da Jigawa tare da Jos. Ka ga jiha shida kenan, don mu gwada wannan noma na damina, mu ga karɓuwarsa. Daga bisani sai mu buɗa zuwa wasu ƙasashen mu gani. Ka ga za a noma alkama sau biyu kenan a shekara, kamar yadda ake noma shinkafa.

Waɗanne matakai kuke bi wajen ba wa manomanku horo a wajen noma a ƙasar nan?
To, akwai matakai da yawa kamar yadda ka sani Kowacce jiha muna da shugabanni, kuma su ne suke da alhakin nusar da manoman alkama game da hanyoyin da za su bi wajen inganta nomanta. Kamar idan ka ɗauke ni a matsayin shugaba na ƙasa, na fito daga Jahar Jigawa. Sai mataimakana guda uku daga sassa daban-daban. Mataimaki na musamman kan harkar noman alkamar daga Jihar Bauchi yake. Sai kuma mataimaki a kan sarrafa ita kanta alkamar daga Birnin Kebbi. Mataimakina kuma na uku daga Jahar Kano a kan harkokin kasuwanci. Wanda kuma kowanensu ya ƙware kan abinda aka ɗora shi kansa dan bunƙasar da ake samu kan noman alkama yau da gobe. Don haka mun raba muƙamin da kowanne zai kula da ɓagaren da ya fi sani a kansa. Haka mu ƙofarmu ta manoman alkama buɗe take. Kuma ba ma karɓar Naira goma. Abinda muke buƙata shi ne, ka zo ka ce za ka yi noman mu ɗauki duk abinda ya kamata na rajista idan Allah ya sa mun tura sunanka CBN,  su kuma suka maido mana sunanka da cewa ka cancanta a ba ka bashi, to lokaci ne. Za mu ce ka zo ka biya kuɗin rajista, sannan mu ba ka kayan noma ka je ka cigaba da nomanka. Abinda ya sa muke haka shi ne, wannan dubu ɗayar zuwa biyu idan ya ba ka ka kasa sama masa, sai ka ga ta zama fitina. Sannan za ka iya ɗaukar kayan noman ka ba mutum ya tafi kuma ba manomin ba ne. Amma idan shi ya kawo kansa aka tantance shi, ka ga babu shamaki sai a taimaka masa. Yanzu muna da manoma sama da dubu ɗari uku da suka yi rajista da mu, kuma muna sa ran samun manoma sama da miliyan biyu da rabi don cike wancan giɓin da ake son cimmawa. Don haka, mun ɗauki dabaru da yawa don ganin mun inganta harkokin noma duk da cewa za ka ga mutane da yawa sun fi ka dabaru.

Wacce godiya za ka yi ga gwamnatin Tarayya ganin irin hoɓɓasa da ta yi don bunƙasa harkar noman alkama? 
farko godiya ta musamman ga mai girma Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya yi wannan namijin ƙoƙari da tunani don ganin an tallafi talaka da abinci. Wannan za mu iya cewa wata baiwa ce da Allah ya ba Muhammadu Buhari na ganin ya ciyar da ƙasar nan da abinci. Sai godiya ga shuwagabannin babban Bankin ƙasa da suka yarda tare da fiddo tsarin, tare da ba da bashin har ya zuwa karɓar bashi don taimkon jama’armu na ƙasar nan. Sai godiya ga gwamnonin da ake noma a jiharsu. Don idan ba su amince ba, to babu wanda zai fito daga wata jihar har a samu nasara. Sai godiya ga sauran shugabannin jihohi. Da babbar godiya ga su kansu manoman da suka yarda suka fito aka basu kayan suke nomawa tare da maido abinda aka ba su ba tare da son zuciya ba. Saboda kowa ya san bashi na da daɗin karva tare da wahalar mayarwa. Dan haka, muna godiya matuƙa bisa ga namijn ƙoƙarinsu wajen riƙe wannan amana.

Wacce shawara kake ganin za ka iya bayarwa a game da noman alkama a ƙasar nan?
Na farko, dole sai mutum ya zama jajirtacce kuma mai riƙon amana da gaskiya. Idan an ba mutum, ya san an bashi, ya kuma ƙoƙarta maidowa. Sannan idan mutum ya yi asara, to ya san da sanin cewa, ya yi asara. Abinda ya kamata a taimaka masa ta hanyar inshora don rage raɗaɗin abinda ya rasa. Sai kira ga gwamnati da ta duba yadda aka samu kai na rashin abinci tare da duba yadda za a bijiro da wasu hanyoyin bunƙasa noman alkama a wannan ƙasa. Sannan kuma a samu wata yarjejeniya da gwamnati za ta sa wa hannu na tsawon shekaru biyar don fita daga wancan ƙangin na fidda maƙudan kuɗaɗe wajen shigo da alkamar waje, da za su ishe mu a bunƙasa nomanmu a cikin gida, da ba ma lallai a kashe duk kuɗaɗen da ake fiddawa ba zuwa wasu ƙasashen don fita daga ƙangin yunwa da zaman banza.

To, mun gode.
To, ni ma na gode, Allah ya ɗaukaka wannan gidan jarida na Blueprint Manhaja.