Zagin addini wani: laifin iyaye ko ‘ya’ya (2)

Daga AISHA ASAS

Mai karatu barkanmu da ganin zagayowar sati lafiya. Sannunku da jimirin bibiyar jaridar Manhaja. Allah ya zaunar da ƙasarmu lafiya. A wannan satin za mu ci gaba daga inda muka tsaya daga darasin da muka fara shimfiɗa a satin da ya gabata.

Kirista na da muhimman mutane da yake darajawa da ko sunansu zai faxa yakan faɗe su da mutuntawa, don haka Musulmi ya kamata ya guji aibata su duk da cewa shi bai yarda da matsayin da suke ba su ba. Shima Musulmi yana da irin mutanen da yake ba wa girma da daraja, don haka Kirista sai ya guje ambato su da mummunar kalma, ba wai don yarda da darajarsu ba, sai don zaman lafiya.

Nijeriya dai uwar Musulmai da Kirista ce, kuma bata tava faɗar ta shirya ‘sheganta’ ɗaya daga cikin ‘ya’yanta ba, don haka zama tare ya zama tilas, idan kuwa haka ne me ya kamace mu da ya wuce neman hanyar zama tare ba tare da ɗaya ya ɗaga makami ga ɗaya ba, mafitar kuwa iyaye ne, domin su ne za su iya wannan aikin.

Ban ga fa’idar zagin addinin wani ba bayan akwai hanyoyin da za ka iya wa’azi cikin lalama ga wanda ba ya cikin addininka, har hujjojin ka su yi tasiri ba tare da ɓangare ɗayan ya ganshi a matsayin cin fuska ba.

A duk inda kaga ana faɗan addini a Nijeriya za ka tarar da ƙiyaya ce ta haddasa shi, kuma ba wanda yake ci sai mu da muka assasa fitinar. Idan mun kammala, mu ɗin ne dai za mu kwashi gawawaki mu bine, mu fara neman kuɗaɗen gyaran gidajen da muka ƙone.

Shi fa addini ra’ayi ne, ba ta inda aka ce dole sai ka yarda da wani ko sai ya yarda da na ka, idan kuwa haka ne, mene ne naka na shia gonar wani, ya riƙe nasa da kuma mutanen da yake mutuntawa, ya daraja su ya kuma yi ta maimaita su a bautarsa, ni kuma inkame bakina daga aibata su ko damuwa da irin soyayar da yake nuna masu, ni ma in aikata hakan gare shi. Ban yarda da na ka ba, amma ina mutunta zaɓinka don kana ɗan ƙasata, me kake bautawa kai dai ke yi ba ni ba, don haka ba ruwa na da sha’anin addininka, mu yi mu’amalar da ta haɗa mu, idan lokacin ibada ya yi, kowa ya tafi inda ya yarda da shi. Hakan ne zai kawo zaman lafiya da kawar da tashin hankali.

Ban taɓa jin addinin KIrista ya yi koyi da tashin hankali ba ko ya ce ku tokane wani addini ba, haka shima addinin Musulunci bai ba wa mabiyansa damar tada fita ba, duk da cewa an samu wasu ɓara gurbi da ake amfani da su ana shafawa addinin Musulunci baƙin fenti, sai dai zuwa yanzu anyi walƙiya, gari ya yi haske, domin duk wanda ya yarda taaddacin da ake yi Musulunci ne, to ya jahilci addinin ko kuma yana bin ra’ayin wani ko shi ne karan kansa ne ba ya son gaskiya, idan kuwa haka ne, to ta ina ake samo ƙiyaya da tokanar juna da ya wuce tarbiyyar iyaye.

Muna da matsalolin da ya kamata kowannen mu ya duƙufa neman taimakon ubangijinsa sauƙi ba wai mu tsaya tokanar juna ba. Da kai Musulmi da Kirinsa duk matsalar tsaro da tsadar rayuwa ta shafe ku, to me ya kamace ku gabaɗaya da ya wuce neman taimako da duƙufa da addu’a a Msallatai da Coci don ganin mun ga ƙarshensu ba su ga ƙarshen mu ba.

Masu waɗannan matsala idan sun koma aibata junansu da suke aiki tare ko kasuwanci ko karatu to fa alama ce ta rashin sanin ciwon kai. Shi fa zaman lafiya aka ce yafi zama ɗan sarki. Kamata ya yi ko faɗa mu ke son yi, kowa ya fito da makaminsa tsakanin Musulmai da Kirista mu haɗa kai mu je mu yaqi masu cin zarafin matanmu da kashe mazajenmu tare da kwashe dukiyoyinmu.