Lafiya Jari: Tarin jini

Spread the love

Tare da MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

Kamar yadda taken wannan rubutun ya ke, tarin jini shi ne mutum idan ya yi tari sai jini ya fito a madadin ya ga majina. 

Tarin jini yana fitowa ne daga huhu ko kuma hanyoyin iska da suke kaiwa izuwa huhun. 

Tarin jinin zai iya kasancewa kaɗan, matsakaici ko kuma mai yawa, wanda ya ke jefa rayuwar marar lafiyar cikin garari. 

Yadda za a gane wannan jini daga hanyar iska ya ke (ba daga hanyar abinci ba, wato aman jini) shi ne za a ga kumfa a cikin jinin kuma launinsa ja ne irin jajur ɗin nan.

Tarin jini mai yawa zai kawo:

1. Toshewar bututun iska a maƙogwaro.

2. ƙarancin iskar oksijin da ke zagayawa jiki.

3. ƙarancin jinin da ke zagayawa a jiki (idan an yi tarin jinin da yawa).

Abubuwa da yawa na kawo tarin jini, amma kafin na yi bayaninsu, ya kamata mu san cewa, maras lafiya mai fama da tarin jini zai iya kasancewa ya na fama da wasu alamun irinsu: 

Ciwon ƙirji

Tari

Kasala

Saurin gajiya

Da sauransu

Abubuwan da ke kawo tarin jini:

1. Jin ciwo a hanyar wucewar iska, imma mutum ya yi raunin da kansa ko kuma wani daban ya yi ma sa raunin. Misali; shigar baƙon abu hanyar iska, yi wa mutum rauni lokacin sa robar hanci, shigar wani abu mai kaifi da makamantansu.

2. Harbuwar hanyar iska da ƙwayar cuta. Misali; lumoniya da tarin fuka (TB).

3. Gudan jini a cikin hanyoyin jini da suke kai wa huhu jini.

4. Matsaloli da suka shafi jini. Misali; tsinkewar jini ko kuma daskarewarsa a cikin jiki

5. Ciwon daji.

Tarin jini na nuni da cewa, akwai matsala a huhun mutum ko hanyoyin iska ko hanyoyin jini, ko kuma zuciya. Saboda haka yana da kyau maras lafiya ya ga likita akan lokaci. 

Ku tara a rubutu na gaba da yardar Allah.

Naku, MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

By ukarofi