Ƙungiyar IPI ta buƙaci a tuhumi jami’an tsaron da suka buɗe ma ƴan jarida masu ɗaukar zanga-zangar yunwa wuta.
Ƙungiyar ta faɗi haka ne da kakkausar murya a dalilin buɗe ma ƴan jarida wuta da jami’an su ka yi a filin wasa na Moshood Abiola, inda ƴan jaridan suka sha da kyar, amma harsashi ya fasa motar wani daga cikin su.
Wannan lamarin yayi muni saboda hakan ya faru ne, washegari da hafsan sojojin Nijeriya ya ce ƴan jarida su daina yaɗa zanga-zangar.
Harbin yan jarida a yayin da suke bakin aiki ba dimukraɗiya bane, dole a ɗau mataki a kan su domin ba ƴan jarida kariya yayin da suke bakin aiki.
