DSS ta kama jagoran zanga-zangar yunwa a Abuja

Spread the love

Rundunar ƴan sandan farin kaya sun kama ɗaya daga cikin jagororin zanga-zangar yunwa a Abuja, Micheal Lenin.

Rahoton da Blueprint Manhaja ta samu shine hakan ya faru ne karfe biyu na safiyar ranar litinin, inda suka ɗauke shi a gidan shi da ke unguwar Apo a cikin babban birnin tarayya Abuja.

Daraktan “Take it back movement” Damilare Adenola, ya tabbatar da faruwan haka, kuma ya ƙara da cewa jami’an sun ci zarafin Micheal a gaban iyalansa kafin su tafi dashi.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, an kasa samun kakakin rundunar ƴan sandan farin kaya,
Peter Afunaya a wayar salula. Kuma bai maido amsar saƙonni da aka tura ma shi ba.

By ukarofi