Gobara ta ƙone rijiyar man NNPCL

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Hukumar kula da tace man fetur ta NUPRC, ta ce sun samu rahoton kamawar gobara a rijiyar Akaso mai baki huɗu da kamfanin NNPC ke gudanarwa a ranar Asabar.

Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Laide Shonola ya fitar a ranar 3 ga watan Agusta ta ce, lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 11:12 na dare a ranar Juma’a inda gobarar ta faɗaɗa zuwa rafin da ke kusa da wajen.

Shiyyar gudanarwa ta 18 ta NNPC ta tabbatar da cewa an samu ɗaukin gaggawa domin kashe gobarar da kuma keɓance wajen ta hanyar amfani da wasu sinadarai da ke hana bazuwarta zuwa wasu wurare.

Haka nan, sanarwar ta ce su na ƙoƙarin maye gurbin man da aka rasa inda tuni su ka aika jirgin ruwan kamfanin da kuma jami’an sanya ido domin kulao da yanayin wajen.

Kawo yanzu dai, ba a gano dalilin aukuwar lamarin ba wanda a halin yanzu ta naɗa kwamitin bincike da ya ƙunshi masu-ruwa-da-tsaki domin gano musabbabin aukuwar lamarin.

By Babaji