IBB ya musanta zargin neman dawo da mulkin soji a Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Tsohon shugaban ƙasa na mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya musanta zargin cewa ya na son a dawo da mulkin soji a Nijeriya, ya na mai cewa demokraɗiyya ta na nan daram.

Wata sanarwa da aka wallafa a shafin X, ta ce IBB ya ce, “Nijeriya ta kasance cikin yanayi mafi kyau a lokacin mulkin soji yayin da mulkin demokraɗiyya ya haifar da sanya ƙasar cikin ƙunci.”

Sai dai wata sanarwa daga ofishinsa na yaɗa labaru mai ɗauke da sanya hannun Mahmud Abdullahi ta ce, Janar Babangida bashi da shafin X, ya na mai jaddada soyayyarsa ga tsarin demokraɗiyya da Nijeriya ke kai inda ya yi kira ga ƴan Nijeriya su ba ta haɗin kai wajen ganin ta kai ga gaci.

Haka nan, sanarwar ta shawarci al’umma da su ƙaurace wa duk wani jawabi daga X da aka ganganta ga Janar Babangida, ta na mai cewa ƴan jarida da masu amfani da kafafen sadarwa su ke tabbatar da gaskiyar labari kafin su yaɗa shi.

Nijeriya ta kasance ƙarƙashin mulkin soji na kusan shekaru 30 tun daga lokacin samun ƴanci a shekarar 1960, wanda soji takwas ne su ka mulke ta ciki har da Janar Babangida a tsakanin 1985 da 1993.

By Babaji