Zanga-zanga: Gwamnatin Kaduna ta sa dokar hana fita a Kaduna da Zariya

Spread the love


Daga USMAN NASIR KAROFI

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanya dokar hana zirga-zirga tsawon awa 24 a biranen Kaduna da Zariya. Hakan ya biyo bayan taron majalisar tsaro ta jihar da ya wakana a yau Litinin.

Sanarwa, wacce kwamishina mai kula da Ma’aikatar Tsaro da Gida, Samuel Aruwan, ya fitar ta ce, an samu hujjoji masu ƙarfi da ke nuni da cewa ɓatagari sun shiga cikin zanga-zangar lumana da ake yi. Hakan ya sanya sun kai farmaki da dukiyoyin al’umma da dama a jihar.

A dalilin wannan, majalisar tsaro ta jihar ta ga ya dace a sanya dokar hana zirga-zirga a faɗin cikin garin kaduna da Zaria.

Sanarwar ta shawarci yan gari da kowa ya zauna a gida domin barin jami’an tsaro suyi aikin su.

By ukarofi