‘Yan sanda sun kama mutane 64, sun ƙwato kayan da ɓata-gari suka wawashe a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Rundunar ƴan sanda a jihar Katsina ta ce ta kama matasa 64 da suka sace kayan jama’a da na gwamnati ciki har da buhunan takin zamani 693 bayan da ɓata-garin suka ɓalle ma’ajiyar gwamnati a yayin gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa da rashin tsaro da ta rikiɗe zuwa tarzoma a jihar.

Kakakin rundunar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyanawa manema labarai hakan a birnin Katsina.

Tun farko, rundunar ta fitar da wata sanarwa inda ta yi kira ga iyaye akan su kula da ƴaƴansu tare da jan kunnensu kan su guji shiga ayyukan da suka saɓa wa doka da suka haɗa da; shiga zanga-zangar tarzoma, ɓarnata kayan jama’a da kuma wawashe dukiyar gwamnati ko ta al’umma.

Sanarwar ta kuma buƙaci matasan da su kasance masu kamun kai tare da ƙin yarda ayi amfani da su wajen tayar da tarzoma ko rikici.

A cewar kakakin rundunar, hukumar ƴan sanda tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro, za su riƙa gudanar da sintiri akai-akai domin tabbatar da bin dokar hana fita da aka sanya a faɗin jihar.

Kazalika, rundunar ta yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu da karya dokar, za a hukunta shi yadda ya dace.

By Babaji