LAFIYA UWAR JIKI: Illolin aikata istimna’i (masturbation) kashi na biyar

Illarsa ga al’aura (2)

A rubutun da ya gabata na kawo illolin aikata istimna’i ga al’aurar namiji. Zan ƙarasa, sannan kuma mu kalli illolin da zai iya haifarwa ga al’aurar mace. 

Abinda na sani shine duk wata jijiyar da ta ke tsarto ruwa a jikin ɗan adam tana tsira ne daga barazanar ciwon daji (kansa) matuƙar ta na tsarto da ruwan da Allah ya tsara ta fitar.

Misali; akwai halittu a cikin maman mace da suke da alhakin samar da ruwan nono. Macen da ba ta taɓa shayarwa ba, ta fi shiga haɗarin kamuwa da kansar mama fiye da wadda ta taɓa shayarwa; namiji da yake fitar da maniyyi daga lokaci zuwa lokaci ya fi aminta da kuɓuta daga kansar maraina (prostate) fiye da wanda ya tara maniyyi bai fitar da shi ba. 

Amma a yadda na fuskanta a nazarin da na ke yi, akwai wata ɓoyayyiyar alaƙa tsakanin kansar maraina da yawan istimna’i. Wataƙila nan gaba idan bincike ya yi nisa a gano gaskiyar lamari. Wannan hasashe ne kawai, saboda ana can ana tafka muhawara akan wannan.

A ɓangaren mata kuwa, shigar da sandararrun abubuwa domin gamsar da kai ya na da haɗarin kawo shigar ƙwayar cuta (infection), wanda abu ne mai wahalar sha’ani sosai. Idan ana amfani da kayan itatuwa irinsu ayaba ko kokomba ko karas, musamman idan ba a wanke su da kyau ba, to sinadarin da manoma suka fesa musu, ko kuma dattin ƙasar wajen da aka girbe su za su iya maƙalewa a jikin ɓawonsu. Idan aka yi istimna’i da su kuwa sai a samu shigar ƙwayar cuta.

Yawan amfani da abubuwa domin gamsar da kai zai iya sa wa gaban mace ya daina jin daɗin mazakutar namiji. Irin waɗannan mata namiji ba zai taɓa gamsar da su ba, saboda gamsuwar da su ke samu da istimna’i ya ninka gamsuwar da suke samu daga namiji. Sun sabar wa gabansu shigar sandararrun abubuwa a maimakon zakarin namiji, kamar yadda Sarkin Halitta ya tsara. 

Haka kuma bincike ya nuna yawan durza ɗan tsaka (clitoris) ya na lalata wayarin (nerɓe supply) da Allah ya yi masa. Ita wannan halitta, tana saman ƙofar shiga gaban mace, kuma ta na jin taɓi sosai fiye da ko ina kaf jikin mace (the most sensitiɓe part of the female body). Idan aka lalata shi ta hanyar da ba ta dace ba, to babu shakka ƙarfin gamsuwa da za a samu daga saduwa zai ragu sosai da sosai.  

Naku, Mustapha Ibrahim Abdullahi

©MIAbdullahi 2024