Arewa: ba ta san ciwonta ba balle ta yi wa kanta magani

Daga ALI ABUBAKAR SADIƙ 

Duk yadda wani, wata ko wasu za su yi ƙoƙarin siffanta surarka, wato fari ne kai ko baƙi, kyakkyawa ko mummuna, ba zai  kai kallon kanka sau ɗaya ba a madubi.

Wani abu da ya faru ranar jajiberen zaɓen ƙananan hukumomi a Jihar Kano makon da ya gabata, ya daɗa tabbatar min da hakan. Wato abokina, Hamisu Lamiɗo Iyantama, shahararren jarumi kuma mai shirya fina-finan Hausa, wanda ke da dubban mabiya a shafinsa na Facebook, ya yi wata tambaya a shafin nasa, inda yake neman shawarar mabiyansa. Wato a zaɓen da za a yi washegari, ya na fuskantar tsaka mai wuya, domin jam’iyyar APC ta tsayar da ƙaninsa ɗan takarar Shugaban ƙaramar Hukumar Dala, yayin da Jam’iyyar NNPP ta tsayar da abokinsa; shin wa ya kamata ya zaɓa?

Da na bibiyi dukkan albarkacin bakin waɗanda suka tofa albarkacinsu na gudunmuwa, sai na ga kaso 99% su na ba shi shawarar kawai ya zaɓi ƙaninsa. Babu wanda ya ce masa ya duba cancanta. Wato son kai, ninanci, shine babbar annobar da ta mamaye tunanin ’yan Arewa tun tale-tale kuma ta zama tarnaƙin da ya hana mu ci gaba ko iya maganin matsalolonmu.

Idan muka duba tarihi, za mu fahimci cewa, Turawa ne ummul-aba’sin ɗora mu kan wannan hanya, domin da zuwansu, da ƙarfin tsiya suka haɗa aurenmu da Kudancin Nijeriya a 1914, da zummar amfani da hakan, domin tatsar arzikinmu zuwa ƙasashensu da kuma bautar da mu har bayan sun ba mu ’yancin kanmu.

Bayan samun ’yancin kai,  rarraba ƙasar zuwa yankuna uku ya haifar da tsere da nuna bambanci tsakanin juna wajen shugabanni irinsu Awolowo, Azikwe da Sardauna a ƙoƙarin gina yankunansu. Wannan tsari daga ƙarshe ya kai ƙasar ga yaƙin basasa.

Bayan kaucewar shugabannin farko bayan samun ’yancin kai, sai aka sami tasowar wasu muggan ’yan boko (sojoji, ma’aikata da ’yan siyasa), waɗanda suka mayar da ninanci ya zama abin bautarsu, yadda su ka bazama da satar dukiyar al’umma, domin gina kansu da ya-nasu-ya-nasu. Hakan kuma ya kwanto kurar da ta yi kaca-kaca da Arewa, wato cin hanci da rashawa.

Duk wanda ya haura shekaru 40 zai iya tuna Arewa irin ta da, wacce ake zaune lafiya da kishin juna kafin a rusa komai. Sannan samuwar sabbin malamai makwaɗaita masu bin mahukunta, ya haifar da auren da ya gama rusa Arewa.

A duk lokacin da al’umma ta zamto babu cancanta a kan gaba wajen samar da shugabanni, muƙamai, ayyukan yi da zamantakewa, ya zamana sai wa ka sani, haƙiƙa ɓalɓalcewa ta zo wa wannan al’umma.

Babu dalilin da Arewa za ta zama yadda ta ke a yau ba, domin wannan ɗabi’a ta ninanci da ta zamar mana iskar shaƙa ba, tun daga kan shugabanni zuwa ga mafi ƙarancin talaka.

Matuƙar ba za mu yi zamiya mu koma kan cancanta da haɗin kai da sadaukarwa ba, haka za mu ci gaba da zama a rayuwar da gara ta dabbobi, domin ko dabba na ƙoƙarin kauce wa duk abinda ta ga zai cutar da ita. Amma mu a yanzu idan “jifa ya wuce kanka, ya faɗa kan uban kowa”.

Ni da kai, da ita da su, yau a Arewa ba za mu iya haɗuwa, domin magance matsalar kwatar unguwarmu ba. Ba wata matsala, komai girmanta a yau da za ta addabi Arewa mutanen Arewa su haɗu waje guda su tabbatar sun kawar da ita. Cikakken misali nan kusa shine matsalar wutar lantarki da ta faru a watan nan. Ka ga wani gungu na mutanen Arewa sun yi wani hobbasa?

Taron ƙungiyar Arewa ta ACF bai wuce na shan shayi da fitar da doguwar takarda ta matsayar bayan taro ba, wacce a kullum babu komai cikinta illa mun cimma matsayar za a yi kaza-da-kaza, wanda a cikin kaza da kaza ɗin ba za ka sami guda ɗaya da ya bijiro da wata manufa, wacce za ta kawo maslaha ta kai tsaye nan take ba. Sai dai kawai kuma a watse a ci gaba da sauraron zuwan wata sabuwar matsalar kafin a sake kiran wani taron na shan shayi.

Idan ba mu yi azamar gane cewa, ba mu da wani maƙiyi da ya wuce karan kanmu ba, wallahi ba mu kama hanyar magance matsalolinmu ba, domin wanda bai san inda ciwo ya ke ba, ta ina zai sami maganinsa?